Ko Tinubu ya fara yakin neman zaben 2023 daga Jihar Kano ne?

Tinubu da Ganduje da Sarkin Kano

Asalin hoton, Aminu Dahiru SSA Photography to the Kano State Gov

Masana harkokin siyasa a Najeriya sun fara tsokaci kan bikin zagayowar ranar haihuwar Sanata Ahmad Bola Tinubu, jigo a jam’iyyar APC mai mulki da za a yi a Jihar Kanon Najeriya.

Wannan ne karon farko da ake yin bikin a wata jiha da ke arewacin Najeriyar, inda a baya an fi yin bikin a mahaifar Tinubu wato Legas.

Gabanin taron, Tinubu ya kai ziyara tare da duba wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Kano ta yi, sannan ya gana da ƙabilun yankin kudancin kasar mazauna Kano da kuma wasu daga cikin malaman addinin Musulunci.

Kafin zuwansa Kano, Tinubu ya je Jihar Katsina a makon da ya gabata, har ma ya bai wa ‘Ć´an kasuwar da gobarar babbar kasuwar jihar ta shafa tallafi.

A na sa ran manyan Ć´an siyasa daga jam’iyyar APC da masu riĆ™e da muĆ™amai daga sassan Ć™asar daban-daban za su je Kano don halartar wannan biki.

Sai dai mai bai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa rashin kyawun yanayi ya hana wasu manyan ƙasar da dama tafiya Kanon.

Ya ce: “Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Asinbajo, da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila da ni kaina ba za mu samu damar halartar taron ba, sakamakon rashin kyawun yanayi da ake fama da shi a Kanon, dalilin da ya hana tashi da saukar jiragen sama.”

Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa ne a kwalejin share fagen shiga jami’a ta CAS a Kano, yana da ra’ayin cewa lallai da walakin goro a miya.

Asalin hoton, Aminu Dahiru SSA Photography to the Kano State Gov

A cewarsa: ”Bisa al’ada a birnin Lagos ake yin bikin, amma abin mamaki bana an kawo shi arewacin Najeriya kuma a Jihar Kano, wannan ya nuna tabbas akwai alaĆ™a ta manufar Tinubu ta yada manufar siyasarsa a shekarar 2023, a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulki”.

Kabiru Sufi ya ce tuni an samu masu sukar matakin, wadanda suke ganin a baya-bayan nan da aka yi ta samun tashin hankali a yankin Yarabawa Tinubu bai ce komai ba, alhalin yana daga cikin masu karfin fada-a-ji a yankin nasu.

Bayanan hoto,
Ana alakanta ziyarar ta Tinibu da kaÉ—a gangamin siyasar shekarar 2023, inda ake tsammanin zai tsaya takarar shugaban kasa

”Wannan ya nuna lallai akwai siyasa a lamarin, kuma ana ganin zabar arewa da ya yi ba lallai ‘yan arewa su yi murna da shi ba.

“To amma wasu na ganin an fito da muhimmancin Jihar Kano a siyasar arewacin Najeriya, tun da har Tinubu ya zabe ta a matsayin inda zai fara kada gogen share fagen siyasar 2023,” in ji Sufi.

Masu lura da al’amuran yau da kullum ba su yi mamakin goron gayyatar da aka bai wa Tinubu zuwa Kano ba, ganin cewa da ma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na goyon bayansa, sannan ba za a gane tasirin taron ta nasara ko akasin haka ba sai an kammala shi da kuma abin da ya biyo bayansa.

Malam Kabiru Sufi ya ce ziyarar da Tinubu ke kai wa jihohin arewacin kasar duk na daga cikin zawarcin kuri’u na al’ummar yankin.

Menene alfanu da nakasun wannan ziyara ga jam’iyyar APC?

”Hakan zai iya zama alfanu ko naĆ™asu ga ita jam’iyyar APC, musamman idan jam’iyyun adawa suka tsaya tsaf suka dubi al’amarin suka yi wani shiri da zai ba su riba, sabanin wanda APC ta fara yi a yanzu, to zai iya zama nakasu a gare ta,” in ji Kabiru Sufi.

“Amma idan fara shirin da suka yi da wuri bai sa jam’iyyun adawa sun farga sun fara nasu shirin ba, to APC za ta ci nasara da gajiyar wannan taro da na murnar zagayowar ranar haihuwar shi Bola Ahmad Tinubu a jihar Kano.

“Amma su kansu jam’iyyun adawar za su iya amfani da damar da suke da ita, idan aka yi la’akari da rarrabuwar kawuna da barakar da ke cikin jam’iyyar APC, za su iya cin gajiyar hakan,” in ji Kabiru Sufi.

Me Ć´an Najeriya ke cewa kan cikar Tinubu shekara 69?

Tun da sanyin safiyar Litinin, shafin sada zumunta na Twitter ya É—auki batun cikar Bola Tinubu shekara 69 a duniya baki É—aya.

An Ć™addamar da maudu’i mai taken #Jagaban da kuma #TinubuIsKey, aka yi ta amfani da su wajen taya shi murnar cika waÉ—annan shekaru.

Wasu sun yi ta kuranta shi, wasu kuma suna amfani da damar wajen sukarsa.

Akasarin saƙonnin da mutane ke wallafawa a shafin suna nuni ne da cewa suna fatan shi ne zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023, kuma suna maraba da hakan.

A hannu guda kuma, akwai masu rajin cewa bai kamata matasa su zaƙe wajen assasa batun tsayar da Tinubu takara a shkearar 2023 ba, inda suke cewa lokaci ya zo da ya kamata a bai wa matasa dama su karbi ragamar mulkin.

Ga dai abin da wasu ke cewa:

@apro_dawildcat ya ce: “Barka da zagayowar ranar haihuwarka Asiwaju na Lagos, Jagaban É—in Lagos, jagoran siyasar yammacin Najeriya: shugaban jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Allah Ya ja kwana.

@IsaTochukwu ya ce: “Asiwaju na Lagos. Allah Ya kara maka kwanciyar hankali, tausayi da nutsuwa a yanzu da koyaushe. #Jagaban@69!

@Okeydegeneral ya ce: Ćłan Najeriya ba su san kansu ba! A watan Oktoban bara lokacin zanga-zangar #EndSARs, duk batun da ake yi ba yadda matasa da jam’iyyunsu za su mamaye zaÉ“ukan 2023 ba ne.

“Bayan wata biyar sai ga shi ana ta zancen Jagaban Bola Ahmed Tinubu da Atiku da sauransu. Har yanzu ba mu koyi komai daga shekarar 2015 ba.”

(BBC Hausa)

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...