Ko Sanata Kabiru Marafa zai sake yi wa APC tsakiyar da ba ruwa a Zamfara?

Abdulaziz Yari da Marafa

Taƙaddama jam’iyyar APC na ci gaba da zafi a jihar Zamfara inda ɓangaren sanata Kabiru Marafa ya yi barazanar zuwa kotu idan har uwar jam’iyyar ta sanar da halaccin zaɓen shugabannin mazaɓu da ɓangaren gwamna Matawalle ya gudanar.

A ranar Asabar ne, ɓangarorin APC a Zamfara suka gudanar da zaɓe falle biyu na shugabannin mazaɓu na jam’iyyar, makonni ƙalilan bayan sauran jihohin ƙasar sun yi nasu.

Zaɓen ya sake fito da ɓarakar da ta bayyana ne tun bayan komawar Gwamna Bello Matawalle cikin jam’iyyar mai mulkin Najeriya.

Sai dai kuma shugabancin APC ɓangaren gwamna Matawalle a Zamfara ya ce matakin mazaɓu akwai aka gudanar da zaɓen, kuma sai da suka tuntuɓi dukkanin ɓangarorin jam’iyyar a taron masu ruwa da tsaki da wakilan da uwar jam’iyyar ta turo suka kira kafin gudanar da zaɓen.

Shugaban kwamitin mutum uku da shugabancin Mai Mala Buni ya naɗa Sanata Hassan Nasiha ya ce ba su da masaniyar cewa akwai wani ɓangare na jam’iyyar da ya gudanar da nashi zaɓe a Zamfara.

Amma Sanata Marafa ya ce wakilan da uwar jam’iyya ta tura ba su tuntuɓi ɓangarensa ba ko na tsohon gwamna Abulaziz Yari duk kuwa da matsayinsu na jiga-jigan APC a Zamfara.

Marafa ya ce take-taken da suka gani ne na kokariin yi wa dokoki da ka’idojin zaɓe hawan ƙawara ne ya sa suka gudanar da nasu zaben.

A hirarsa da BBC Sanata Marafa ya yi barazanar cewa abin da ya faru da APC a Zamfara a 2019 zai iya sake faruwa da jam’iyyar a yanzu inda ya ce zai ƙalubalanci sahihancin zaɓen a kotu duk da akwai umurnin wata kotu da ya hana wa ko wane ɓangare tafiyar da jam’iyyar a Zamfara.

“Mu yanzu za mu tafi kotu idan har jam’iyya ta fito ta ayyana cewa ba mu muka ci zabe ba,”

“Duk abin da zai faru sai mun kalubalanci matakin da kuma halaccin shugaban riko na jam’iyyar APC,” in ji Marafa.

Ya kuma yi ikirarin cewa jam’iyyar ta bijerewa dokokinta ne, shi ya sa ya gudanar da nashi zaben shugabanni a Zamfara.

Ya kuma ce APC ta yanke shawarar gudanar da zaɓen ba tare da bayar da kwanakin da dokar zabe ta tanada ba na kwana 21 kafin zaɓe.

Abin da ya faru

Mai Mala Buni ne ya sasanta Abdulziz Yari da Sanata Marafa wanda rikicinsu ya janyo wa APC hasarar shugabanci a Zamfara

Tun da farko a ranar 5 ga Nuwamba uwar jam’iyyar APC ta sanar da dakatar da gudanar da zaɓen shugabanni a cikin wata takarda mai ɗauke da hannun sakataren jam’iyyar na riƙo zuwa ga shugaban kwamitin gudanar da zaɓen Alhaji Ibrahim Kabir Masari.

Kuma takardar ba ta yi cikakken bayani ba kan dalilin dakatar da zaɓen illa a ciki ta ce akwai buƙatar ƙara tuntuɓa.

Daga baya kuma uwar jam’iyyar ta sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen a ranar 13 ga watan Nuwamba maimakon 20 ga wata, kamar yadda ta aikawa hukumar Inec a ranar 10 ga watan Nuwamba, kuma takardar ta nuna Inec ta karɓi takardar a ranar 11 ga wata.

Tun sanar da rushe shugabannin APC a Zamfara da shugaban riƙo na uwar jam’iyya Mai Mala Buni ya yi bayan shigowar gwamna Matawalle cikin APC, jam’iyyar ta sake faɗawa cikin wani sabon rikici a Zamfara.

Matakin bai yi wa ɓangaren tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz da Sanata Marafa daɗi ba, musamman kuma naɗa kwamiti na mutum uku da uwar jam’iyyar ta naɗa bayan rusa shugabannin jam’iyyar.

Wannan ya sa shugabannin APC na Zamfara da aka rusa suka tafi kotu suna ƙalubalantar matakin, inda babbar kotun ta Gusau ta dakatar da ayyukan jagorancin jam’iyyar har sai ta yi hukunci.

Ɓangaren Marafa ya gudanar da na shi zaɓe kamar yadda ɓangaren gwamna Matawalle ya gudanar yayin da kuma tsohon gwamna Abdul’ziz Yari ya ce zai mutunta umarnin kotu.

Idan dai har uwar jam’iyyar ba ta ɗauki mataki ba game da dambarwar siyasar APC a Zamfara, abin da ya faru a zaɓen 2019 zai iya sake faruwa inda jam’iyyar ta rasa shugabancin jihar sakamakon irin wannan rikicin.

More News

‘Gobara ta lalata dukiyar naira tiriliyan uku a Najeriya’

Gobara ta lalata dukiyar da ta kai ta naira biliyan dubu 3, wato tiriliyan 3 a Najeriya, kamar yadda Ministan harkokijn cikin gida na...

Ba Za A Samu Matsalar Karancin Man Fetur Ba – NNPC

Dogayen layuka a gidajen mai na daga cikin alamun da ‘yan Najeriya ke la’akkari da su wajen yiwuwar samun karancin man fetur a kasar. Kamfanin...

‘Ba a cimma matsaya a sulhunta bangaren Ganduje da Shekarau ba’

An kasa cimma matsaya a sulhun da jam’iyyar APC maiu mulki a Najeriya ke ƙoƙarin yi tsakanin ɓangaren gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da...

‘Akwai yiwuwar Najeriya ta ci gaba da ciyo bashi don biyan tallafin mai’

Akwai yiwuwar Najeriya ta ci gaba da ciyo bashi domin ci gaba da biyan tallafin man fetur, a cewar fadar shugaban ƙasa. Mai magana da...