Klopp da Aubameyang sun lashe kyautar Premier | BBC Sport

Premier League

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An bayyana dan kwallon Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang a matsayin dan wasan da babu kamaras wajen taka rawar gani a gasar Premier a watan Satumba.

Aubameyang, mai shekara 30 ya ci kwallo biyar a watan jiya a karawa biyar da ya yi wa Gunners har da wadda ya ci a bugun tazara a fafatawa da Aston Villa.

An kuma bayyana kocin Liverpool, Jurgen Kloop karo na biyu a jere a matakin wanda ya fi kowa yin bajinta a gasar ta Premier a dai watan na Satumba.

Liverpool wadda har yanzu ba a doke ta ba a wasannin Premier bana ta yi nasara a kan Newcastle United da Chelsea da kuma Sheffield United a watan Satumbar.

Kocin dan kasar Jamus ya yi takara da mai horas da Bournemouth, Eddie Howe da na Chelsea, Frank Lampard da kuma Brendan Rodgers mai jan ragamar Leicester City.

Aubameyang ya ci kwallo a karawar da Gunners ta yi 2-2 da Watford shi ne ya farke kwallon da Tottenham ta ci Arsenal da kuma wadda Manchester United ta zura a ragar Arsenal.

Dan wasan tawagar Gabon ya yi takara ne da Trent Alexander-Arnold da Kevin de Bruyne da Son Heung-min da kuma Riyad Mahrez.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...