Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Ronaldo, Kane, Benitez, Favre, Torres, Dumfries, Soumare

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Ronaldo bai nuna alamar gazawa ba

Shugaban Barcelona Juan Laporta na sha’awar hada Cristiano Ronaldo da Lionel Messi su yi wasa a kungiyarsa a kakar wasa mai zuwa, kuma a shirye ya ke ya yi musayar ƴan wasansa biyu domin Juventus ta amince Ronaldo, dan wasan gaba mai shekara 36 ya bar ƙungiyar. (AS – in Spanish)

Manchester City ta ce a shirye ta ke ta miƙa ɗan wasan gaba kuma ɗan Brazil striker Gabriel Jesus mai shekara 24, da Raheem Sterling, da wasan gaba na Ingila mai shekara 26 domin ta cima burinta na daukan Harry kane daga Tottenham. An dai sa wa kane farashin fam miliyan 150. (Times – subscription required)

Manchester United na na kan bakarta ta raba Pau Torres, dan wasan baya kuma dan kasar Spaniya mai shekara 24 da Villareal. (Manchester Evening News)

Rafael Benitez na daf da zama sabon kocin Everton bayan ya sake tattaunawa da masu kungiyar a karshen makon jiya, duk da cewa magoya bayan kungiyar sun nuna rashin amincewarsu. (Mirror)

Crystal Palace kuwa tattaunawa ta yi da Lucien Favre domin y maye gurbin Roy Hodgson amma da alama Everton ma na son daukan shi. (Guardian)

Atalanta na fuskantar matsaloli wajen tsawaita kwantiragin Matteo Pessina, dan wasan tsakiya dan kasar Italiya, bayan da kungiyoyi biyu – AC Milan da Roma su ka bayyana cewa su na bukatar dan wasan mai shekara 24. (Calciomercato – in Italian)

Wolves na sha’awar daukan golan Leicester Danny Ward, mai shekara 27 wanda ya burge matuka a wasannin da ya bugawa kasarsa Wales a gasar Euro 2020 da ke gudana a halin yanzu. (Football Insider)

Antonio Rudiger, dan wasan baya mai shekara 28, na son ci gaba da zama a Chelsea a kakar wasa mai shigowa, duk da cewa kungiyar ba ta nuna sha’awar ya ci gaba da zama a Stamford Bridge ba. (Sky Sports)

Kungiyoyi huɗu – Bayern Munich da Everton, da AC Milan da kuma Inter Milan na takara kan wadda za ta yi nasarar daukan Denzel Dumfries – dan wasan baya dan asalin Netherlands mai shekara 25 daga PSV Eindhoven. (Voetbal International – in Dutch)

Liverpool ta ce ba ta da niyyar sayar da Kostas Tsimikas, dan wasan bayan dan asalin kasar Girka mai shekara 25 duk da cewa wasanni bakwai kawai ya buga wa kungiyar a kakar wasan da ya gabata. (Liverpool Echo)

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...