Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Ramos da Varane da Camavinga da Coman da Messi, Ronaldo da Griezmann

h

Asalin hoton, Getty Images

Ɗan wasan Sifaniya mai shekara 35 Sergio Ramos, zai duba lafiyarsa a Paris a yau Talata gabanin komawa Paris St-Germain bayan bankwana da Real Madrid. (ESPN)

Manchester United ta shirya kashe £50m domin sayen ɗan wasan Real Madrid Raphael Varane, da £25m kan ɗan wasan Rennes Eduardo Camavinga, 18, yayin da take ci gaba da kashe kuɗaɗe wajen sayo ƴan wasa. (Marca via Mail)

Shugaban Bayern Munich Oliver Kahn ya jajirce wajen ci gaba da rike dan wasan Faransa Kingsley Coman a ƙungiyar duk da zawarci da Liverpool ke nuna wa kan dan wasan mai shekara 25. (Mirror)

Paris St-Germain ta bai wa Lionel Messi kwantiragi bayan karewar wa’adin yarjejeniyarsa da Barcelona a makon da ya gabata. Ɗan wasan mai shekara 34 ya taimaka wa ƙasarsa wajen kai wa wasan ɗab da na karshe a Copa America duk da cewa yana cikin rashin tabbas a kungiyarsa.(Mail)

Ɗan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann bai fidda rai ba kan Manchester City a wannan kakar idan suka gagara daidaitawa da ɗan wasan Tottenham Hotspur Harry Kane, mai shekara 27. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Juventus na son sake ɗauko ɗan wasan Manchester United Paul Pogba, a wannan kakar. (90Min)

Liverpool ta sha gaba wajen fafutikar sayen ɗan wasan PSG Kylian Mbappe. Ana dai ci gaba da yaɗa jita-jita kan makomar ɗan wasan mai shekara 22. (ESPN)

Sabon kocin Crystal Palace Patrick Vieira na fatan cimma yarjejeniyar farko da ɗan wasan Scotland da Celtic Ryan Christie. Dan wasan mai shekara 26 ya kuma ja hankalin tsohon kulob din Vieira wato, Nice. (Daily Record)

Kocin Arsenal Mikel Arteta na son ci gaba da rike Emile Smith Rowe duk da nacin da Aston Villa ke nuna wa a kansa. Yanzu haka sun shirya sake kara kudin tayin da suka gabatar na farko da bai samu shiga ba. (Mirror)

Sabon kocin Tottenham Hotspur Nuno Espirito Santo na son dauko ɗan wasan Switzerland. Haris Seferovic. Benfica na son sayar da ɗan wasan mai shekara 29 a wannan kakar. (Mirror)

Tsohon ɗan wasan Manchester City Mario Balotelli ya shirya koma wa Adana Demirspor a Turkiyya. (Goal)

More News

EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuɗaɗe

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa...

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...