Kasurgumin Danfashin Da Ya Addabi Kanawa Ya Shiga Hannu – Musa Majiya

[ad_1]








Wannan shine Hafizu Magaji na Unguwar Tudun Murtala, Kasurgumin dan fashi da makami kuma Hamshakin Dan-Daba da ya addabi mutanen Yankin Tudun Murtala, Rimin Kebe, Kwana Hudu da wasu sassa na birnin Kano kamar su bakin Kasuwa, bakin Zuwo da Jakara. Yana Sata, Kwace har da Kisan kai a lokaci daba-daban.

Ya fada tarkon jami’anmu lokacin da yayi arangama da yan Vigilante da misalin karfe biyun dare yana kokarin fasa wani Shago kuma kafin kama shi sai da ya Sassari Yan Vigilante akalla guda uku kafin a kai ga nasarar chafke shi.

Daga Kakakin Rundunar Yansandan Jihar Kano SP Musa Majia.




[ad_2]

More News

An Jikkata Jami’an Tsaro A Harin Da Ƴan Bindiga Su ka Kai Wa Ayarin Motocin Yahaya Bello

A jikkata wasu jami'an tsaro a wani hari da yan bindiga su ka kai kan jerin ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ranar...

Bala Muhammad ya zama shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP

An zaɓi gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP. Siminalayi Fabura zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers shi ne mataimakin shugaban...

Za mu sake bitar mafi karancin albashi a Najeriya—Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin sake nazarin mafi karancin albashin ma’aikata domin dacewa da yanayin tattalin arzikin kasar nan. A cewarsa, akwai bukatar...

EFCC na zargin tsohuwar ministar mata a mulkin Buhari da karkatar da naira biliyan 2

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta titsiye tsohuwar ministar harkokin mata Pauline Tallen kan zargin azurta kai ta...