Kama Nnamdi Kanu ya jefa IPOB cikin tsaka mai wuya

  • Daga Nduka Orjinmo
  • BBC Abuja
Kafin kama Kanu sai da ya mayar da IPOB ƙungiyar da a ka sani a duniya da ke shirya maci irin wannan a ƙasashen Turai misali a ƙasar Italiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Kafin kama Kanu sai da ya mayar da IPOB ƙungiyar da aka sani a duniya da ke shirya maci irin wannan a ƙasashen Turai misali a ƙasar Italiya

Kama mai fafutukar ɓallewa daga Najeriya Nnamdi Kanu ya jefa ƙungiyarsa cikin ruɗani wanda ka iya kawo ƙarshenta gaba ɗaya.

Shugaban ƙungiyar ta IPOB da ke kudancin Najeriya na son ɓallewa a yankin kudu maso gabashin Najeriya don kafa ƙasa ta daban.

Kuma Kanu ya samu goyon bayan dubban mazauna yankin da ke yi masa kallon gwarzo kuma mai kishin yankin nasu.

Sama da shekaru 10 yana kumfar baki a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta yayin da gwamnatin Najeriya ta riƙa ɗaga masa kafa.

Sai a shekarar 2020 a lokacin da fafutukarsa ta rikiÉ—e, bayan da magoya bayansa suka É—auki makamai ne hukumomi suka fara tunanin taka masa birki.

Ana zargin ɓangaren IPOB da ke ɗauke da makamai da ake kira Eastern Security Network da kisan aƙalla mutun 60 mafi yawancinsu ƴan sanda. Amma sun musanta zargin.

Kama Mista Kanu da aka yi ranar Lahadi kan iya zama wani yunƙuri da zai kwantar da fafutukar.

Hotunan kama shi babu shakka za su kashe ƙwarin gwuiwar mabiyansa.

Asalin hoton, Nigeria presidency

Amma ba shi ne karon farko da aka kama mutumin mai shekaru 53 ba. Sai dai ba kamar a baya ba, a yanzu alamu sun nuna cewa jikinsa ya yi sanyi.

Dama ana zargin Kanu da kankane shugabancin IPOB ba tare da kafa wasu jiga-jigai da za su iya jagorantar ƙungiyar ba a gaba, hakan tasa a yanzu babu wani ƙwaƙƙwaran shugabanci a IPOB.

”Rikici kan kuÉ—i da rashin tuntuÉ“ar masu ruwa da tsaki kan abin da ya shafi kafa É“angaren da ke É—auke da makamai bai yi wa wasu daÉ—i ba, a cewar wakiliyar sashen Igbo na BBC Chiagozie Nwonwu, wanda ya yi hira da Nnamdi Kanu a shekarar 2019 lokacin da ya ke gudun hijira.

Wani wanda ya tsere tare da Kanu bara shi ne mataimakinsa Uche Mefor, wanda shi ya riƙe ƙungiyar a karon farko da aka kama mai gidansu.

Kazalika zargin karkatar da kuɗaɗen tallafi da aka samu ya sa wasu magoya bayan IPOB da ke zaune ƙasashen Amurka da Burtaniya ficewa daga ƙungiyar.

Haka ma IPOB ta samu naÆ™asu sosai a cikin gida, bayan da jami’an tsaro suka fara yaÆ™i da su.

An kashe masu gwammai a ƙungiyar tare da tsare wasu a gidajen yari.

Da sauran rina a kaba

Ana yi wa Mista Kanu kallon wani hatsabibin mutun mai son ta da zaune tsaye, amma yana aron bakin ƴan ƙabilar Igbo da dama ne yana ci musu albasa, don akwai masu riƙe da gwamnatin Najeriya kan yaƙin basasa da aka yi daga shekarar 1967 zuwa 1970.

Ƴan ƙabilar Igbo da dama na zargin cewa ba a damawa da su a siyasar Najeriya. Suna ganin cewa su ke da ƙabila ta uku mafi girma a ƙasar, amma har yanzu ɗan ƙabilar bai taɓa riƙe muƙamin Shugaban ƙasa ba tun shekarun 1960.

Bugu da ƙari suna zargin cewa babu abin da gwamnatin tarayya ta tsinana musu.

Map: Nigeria Igbo states

Wannan zargi ya ƙara zafafa ne tun bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015.

A baya ya yi kalami kan yaƙin basasa yayin da ya ke magana kan murƙushe IPOB a shafinsa na Tuwita, wanda ya sa kamfanin sada zumuntar ya goge kalaman nasa.

Ya kuma taÉ“a cewa ba zai yiwu waÉ—anda suka ba shi kashi biyar na Æ™uri’u ba su yi tunanin za su more shi daidai da wadanda suka bashi kashi 95.

Irin waÉ—annan kalamai daga Shugaban da ba ya da juriyar rashin É—a’a tun a shekarun 1980 sun harzuÆ™a Kanu da ire-irensa.

An fara kama Mr Kanu a shekarar 2015 a lokacin da ya dawo Najeriya, amma hakan babu abin da ya haifar face ƙara masa magoya baya da tagomashi a kudnacin ƙasar.

Za a iya cewa babu wani ɗan ƙabilar Igbo da ake magana a kansa a halin yanzu kamar Nnamdi Kanu, kuma waɗanda suka san shi sosai sun ce dama babban burins hi kenan.

Fitar kutso

Kanu ne ya kafa ƙungiyar tsaro ta Biafra Security Service da a ke kira BSS.

Wata ƙungiya ce da mambobinta ke saka baƙaƙen kaya suna fareti a jihar Abia da ke kudancin ƙasar.

Take-taken shi sun ƙaru, bayan da ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da yunƙurin mayar da Najeriya ƙasar musulmi zalla.

Daga baya ne Shugaba Buhari ya ji cewa tura ta kai bango, kuma bayan da kotu ta bayyana IPOB a matsayin Æ™ungiyar ta’addanci ne sojoji suka dirar wa gidan Mista Kanu a watan Satumban 2017.

Amma ya yi fitar kutso don ba su yi nasarar kama shi ba a lokacin.

Da dama sun yi tunanin an samu sa’ida kan taÆ™addama tsakanin Kanu da gwamnati, amma kuma sai gashi ya É“ulla a Turai a shekarar 2018, inda ya ci gaba da sukar hukumomin Najeriya musamman rikicin manoma da makiyaya.

A bara ne kuma a ka ƙaddamar da zanga zangar EndSars, wadda ke adawa da cin zalin ƴan sanda a Najeriya.

Kuma da dama sun yi amanna cewa boren na daga cikin abubuwan da suka kawo wa Kanu cikas a tasa fafutukar.

Don kuwa bayan da zanga zangar ta rikiÉ—e zuwa rikici, Mista Kanu ya nemi magoya bayansa da su farwa ofisoshin Æ´an sanda.

Wasu kuma na ganin tun bayan farin da aka kai a gidansa a shekarar 2017 ya yanke shawarar bai wa mambobinsa makamai.

Asalin hoton, ESN

Bayanan hoto,
ungiyar tsaro ta Biafra Security Service da a ke kira BSS

A ƙarshen shekarar 2020 ne ya sauya wa ƙungiyar mayaƙan IPOB suna daga BSS zuwa ESN.

Sun kuma riƙa samun horo ne a dazukan kudu maso gabashin Najeriya, inda suke riƙa amfani da bindigogi ƙirar AK-47 da suka sata daga ofisoshin ƴan sanda.

Daga watan Satumban 2020 zuwa watan Mayun 2021 an samu yawaitar hare-hare kan ofisoshin Æ´an sanda da wasu gine-ginen gwamnati kuma kai tsayen hukumomin sun nuna É—an yatsa ne kan IPOB.

Ko a watan Maris sai da sojojin suka tarwatsa sansanonin horon ESN tare da bin sawun kwamandojin ƙungiyar.

Ga mutane da dama musamman matasa da ke tausayawa IPOB, irin yadda sojoji suka saka ƙungiyar a gaba a halin yanzu wata alama ce da ke nuna musu cewa yaƙi ba abu ne da ya kamata su yi maraba da shi ba.

Tun kan a je ko’ina an rufe sana’o’i tare da Æ™aÆ™aba dokar hana fita. Bugu da Æ™ari duk wanda zai ratsa shingen binciken jami’an tsaro dole ya É—ora hannuwansa a kai.

Daga nan ne fa wasu suka fara dawowa rakiyar IPOB da kuma adawa da kama Shugabanta.

Hakan ya sa ake ganin Kanu ya fara shiga jerin masu rajin raba Najeriya da haƙarsu ta gaza cimma ruwa.

Amma da wahala ya zama na ƙarshe, matsawar ba a zauna an tattauna ƙorafe-ƙorafen da da dama a shiyyar kudu maso gabashin Najeriyar ke da su ba.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...