Ka san ‘yan siyasar da ba su taba sauya sheka ba a Najeriya?

Yayin da wannan shekararbNajeriya za ta cika shekara 20 a kan tafarkin dimokradiyya, sauya shekar jam’iyyar siyasa abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya.

Tun bayan dawowar dimokradiya a shekarar 1999 ake samun yanayin da mutane ke fita daga wata jam’iyya su koma wata, musamman tsakanin manyan jam’iyyun kasar PDP da kuma uku wadanda suka hade wato ANPP, ACN da CPC da kuma wani bangare na PDP suka zama APC.

Sai dai duk da haka, akwai wasu manyan ‘yan siyasa da ba su taba sauya sheka ba tun 1999 har zuwa yanzu.

A wannan makala dai mun yi duba ne kan wasu daga cikin wadannan mutane.

Sule Lamido

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Sule Lamido yana daga cikin na gaba-gaba da suka kafa jam’iyyar PDP a shekarar 1998

Yana daga cikin na gaba-gaba da suka kafa jam’iyyar PDP a shekarar 1998, kuma ya yi ministan harkokin waje daga 1999 zuwa 2003 lokacin mulkin Obasanjo.

Ya yi gwamnan jihar Jigawa sau biyu a jere daga 2007 zuwa 2015. Har yanzu shi ne jagoran PDP a jiharsa, kuma bai taba barin wannan jam’iyya ya koma wata ba.

Ahmed Makarfi

Hakkin mallakar hoto
Facebook

Image caption

Ahmad Makarfi tare da Shugaba Muhammadu Buhari

Shi ma ya shiga jam’iyyar PDP ne tun a shekarar 1998. Ya zama gwamnan jihar Kaduna daga 1999 zuwa 2007 karkashin PDP.

Bayan nan kuma sai ya zama sanata a shekarar 2007.

Duk da cewa ya taba shugabantar jam’iyar PDP kuma aka yi ta samun rigingimu kan hakan, bai taba fita daga jam’iyyar don komawa wata ba.

Goodluck Jonathan

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Jonathan ya bai taba fita daga jam’iyarsa PDP

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shi ma bai taba fita daga jam’iyyarsa ta PDP ba, tun daga lokacin da ya kasance mataimakin gwamnan jihar Bayelsa da mataimakin shugaban kasar da kuma yanzu da yake tsohon shugaban kasa.

Abdul Ningi

Abdul Ahmed Ningi fitaccen dan siyasa ne a jihar Bauchi. Ya shiga jam’iyyar PDP tun shekarar 1998.

Tun a 1999 ya shiga majalisar wakilan Najeriya har zuwa 2011. Daga bisani ya zama sanata a 2011 zuwa 2015.

A zaben 2015 ne ya yi rashin nasara, amma har yanzu bai fice daga jam’iyyar ba.

Bola Tinubu Lagos

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tinubu ya yi gwamnan jihar Legas tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007

Fitaccen dan siyasa ne da ba a jiharsa ta Legas kawai ya yi suna ba har a Najeriya baki daya.

Da shi aka kafa jam’iyyar AD a shekarar 1998, bayan dawowar dimokradiya.

Ya yi gwamnan jihar Legas sau biyu a jere daga 1999 zuwa 2007.

Daga baya jam’iyyarsa ta hade da gamayyar jam’iyyun siyasa uku na kasar, inda suka samar da jam’iyar APC.

A yanzu yana daga cikin jiga-jigan APC har ma ana masa lakabi da Jagaba. Kuma bai taba sauya sheka ba.

Kashim Shettima

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shettima yana cikin sawun manyan ‘yan siyasar da ba su taba sauya sheka ba

Gwamnan jihar Bornon Kashim Shettima shi ma yana cikin sawun manyan ‘yan siyasar da ba su taba sauya sheka ba.

Ya yi jam’iyyar ANPP kuma ya koma APC lokacin da jam’iyyarsa ta hade da wasu jam’iyyu gabanin babban zaben shekarar 2015.

Ibrahim Geidam

Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Geidam shi ma yana cikin sawun manyan ‘yan siyasar da ba su taba sauya sheka ba.

Sai dai kamar takwaransa na Borno, ya taba yin jam’iyyar ANPP kafin ya koma APC, lokacin da jam’iyyarsa ta hade da wasu jam’iyyu gabanin babban zaben shekarar 2015.

Sauran sun hada da:

  • Sanata Bukar Abba jam’iyyar APC
  • Ahmad Sani Yariman Bakura na jam’iyyar APC
  • Ibrahim Shehu Shema na jam’iyyar PDP
  • Muntari Shagari na jam’iyyar PDP
  • Abdulkadir Balarabe Musa na jam’iyyar PRP
  • Usman Bugaje na jam’iyyar APC
  • Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP da sauransu.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...