Juyin mulki: Jakadun da Tinubu ya tura don yin sulhu sun isa Nijar

Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na III sun isa ƙasar Nijar don yin sulhu.

Idan ba a manta ba a ƴan kwanakin baya ne dai sojoji suka kifar da gwamnatin shugaba Bazoum, inda ECOWAS ta nuna fushinta tare da ƙaƙaba wa Nijar ɗin takunkumi, ciki har da datse wutar lantarkin da ake ba su daga Najeriya.

A saboda haka ne Shugaba Tinubu ya naɗa Abdulsalami da Sarkin Musulmi don su je su yi sulhu tare da tattaunawa don shawo kan matsalar.

More from this stream

Recomended