Jonathan Ya Ziyarci Ganduje A Gidansa Dake Abuja

Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyar APC na kasa, ya karɓi bakuncin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a gidansa dake Abuja.

An saki hotunan ziyarar ranar Juma’a a shafin jam’iyar APC na X wanda aka fi sani da Twitter a baya.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da aka fitar dake nuna dalilin ziyarar da tsohon shugaban ya kai gidan Ganduje.

More from this stream

Recomended