Wata ƙaramin jirgi ya yi hatsari a unguwar Oba Akran da ke Ikeja a jihar Legas, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.
Kakakin Hukumar Binciken Haɗɗuran Jiragen Sama ta Najeriya (NSIB), Tunji Oketunbi, ya tabbatar da faruwar lamarin a yammacin ranar Talata.
Haka kuma, wani jami’in Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) ya shaida cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.