Jirgin kasan da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja ya buge wata mata dake cikin mota inda hakan yayi sanadiyar ajalinta.
Hatsarin ya faru ne a yankin Kubwa dake birnin tarayya Abuja.
Wani mutum da ya sheda faruwar lamarin ya fadawa gidan talabijin na Channels cewa lamarin ya faru ne bayan da jirgin ya ci karo da motar matar a dai-dai lokacin da take kokarin tsallaka digar jirgin.
Tuni dai jami’an tsaro suka dauke gawar matar tare da motar da ta makale.