Jihar Borno ta tsawaita shekarun yin ritaya na ma’aikatan lafiya

Gwamnatin jihar Borno ta ce an tsawaita shekarun yin ritaya na ma’aikatan lafiya a jihar daga shekarun aiki 35 zuwa 40 ko kuma shekaru 65 na haihuwa.

A wata sanarwa da aka aikewa shugabannin kananan hukumomin jihar, daraktan kula da lafiya a matakin farko, Ibrahim Sheriff ya ce tsawaita wa’adin ya fara ne daga watan Janairun shekarar 2022.

Sherif ya kuma ce gwamnatin ta amince cewa ma’aikatan lafiya da suka yi ritaya kafin ko kuma bayan watan Janairun shekarar 2022 za su iya dawowa bakin aiki.

Tun da farko gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya amince da karin shekarun ritaya na malaman makaranta zuwa shekaru 65 ko kuma shekarun aiki 40.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...