Jihar Akwa Ibom bata taɓa amfana da aikin titi ko da kilomita ɗaya zamanin mulkin PDP

Godswill Akpabio, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ya ce karkashin mulkin jam’iyar PDP jihar bata taɓa amfana da aikin gina titi koda mai tsawon kilomita guda ne cikin shekaru 16.

Akpabio ya mulki jihar tsawon shekaru 8 a karkashin jam’iyar PDP ya kuma kasance a jam’iyar tun daga shekarar 1999 har zuwa lokacin da ya sauya sheka ya zuwa jam’iyar jam’iyar APC a cikin watan Agustan wannan shekara.

Da yake magana lokacin da ya jagoranci wata tawagar dattawan jihar zuwa wurin shugaban kasa Muhammad Buhari, Akpabio ya ce zuciyarsa tana tare da Buhari a zaben shekarar 2015 duk da kasancewarsa dan jam’iyar PDP a wancan lokacin.

Tsohon gwamnan wanda ya kasance shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya ce babu wata sauya sheka da za ta shafi damar da jam’iyar take da ita na cin zaɓe a shekarar 2019.

Akpabio ya cika baki cewa,Akwa Ibom za ta kasance jiha ta farko daga yankin kudu maso gabas da jam’iyar APC za ta lashe zabe a 2019.

Ya ce jam’iyar PDP a Akwa Ibom tamkar gawa ce domin ruhinta ya fita ya zuwa jam’iyar APC.

More News

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

Ƴan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da suka yi bacci a lokacin da suke tsare da mutanen da suka sace

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wasu masu garkuwa da mutane bayan da suka buge da sharar bacci a lokacin da suke tsare...