Jam’iyyar APC Ta Cire Hannunta Daga Zargin Hana Kwankwaso Taro A Eagle Square

[ad_1]








Biyo bayan dambarwar haramtawa Kwankwaso gudanar da taron kaddamar da aniyyarsa ta takarar kujerar shugaban kasa a farfajiyar taro na Eagles Square, jam’iyyar APC ta musanta zargi tare da bayyana cewa ko kadan babu hannunta cikin wannan lamari.

Ko shakka babu an haramtawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, amfani da dandalin Eagle Square wajen gudanar da taron bayyana kudirin sa na takarar kujerar shugaban kasa a ranar Larabar da ta gabata.

Kamar yadda wani jigo na kwamitin yakin neman zabe na Kwankwaso, Kwamared Aminu Abdussalam, ya shaidawa manema labarai na BBC cewa an hana su gudanar da wannan taro bayan tuni sun riga da biyan kudi na hayar farfajiyar.

A sanadiyar haka dole kanwar naki ta sanya Sanata Kwankwaso ya gudanar da taron kaddamar da kudirin sa a wani babban Otel na Achida a ranar Larabar da ta gabata.

A yayin musanta zargi dangane da hannun jam’iyyar APC cikin wannan dambarwa ta haramtawa Kwankwaso amfani da farfajiyar Eagles Square wajen gudanar da taron sa, ta bayyana cewa ko kadan ba ta dahannu cikin wannan lamari.

Jam’iyyar a yayin cigaba da wanke kanta ta kuma bayyana cewa, wannan takkadama tsakanin Kwankwaso ne da kuma kamfanin mai zaman kansa dake kula da filin na Eagles Square da ya hana gudanar da taron.

Kamar yadda shafin jaridar Sahara Reporters ya rawaito, jam’iyyar ta wanke hannunta kan wannan zargi cikin wani sako data bayyana a shafinta na sada zumunta.




[ad_2]

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...