Jami’an zabe a Indonesiya sama da 270 sun mutu yayin kirga kuri’a

Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

Sama da jami’an zabe 270 ne suka mutu a kasar Indonisiya bayan sun tagayyara daga kirga kuri’un miliyoyin ‘yan kasar da suka jefa.

An bayyana cewa akasarinsu sun fara rashin lafiya ne sakamakon dogon lokacin da suka dauka suna kirga kuri’u.

Mai magana da yawun hukumar zaben kasar Arief Susanto ya bayyana cewa akwai kusan jami’an zabe 1,878 da suka fara rashin lafiya.

Irin wannan shine zabe na farko a kasar mai mutane kusan miliyan 260 inda aka hada zaben shugaban kasa da kuma na ‘yan majalisun tarayya na da na yankuna.

An bayyana cewa an hada zabukan ne lokaci guda domin saukakawa gwamnati wajen kashe kudade amma da alamu hakan ya sa jami’an zaben cikin wahala har wasu suka rasa ransu.

Kusan mutum miliyan 64 ne suka jefa kuri’unsu a rumfunan zabe kusan 800,000.

Akasarin wadanda abin ya shafa sun samu aikin ne a matsayin ma’aikatan wucin gadi wadanda ba a yi masu gwajin asibiti ba a ga ko su na da koshin lafiyar aiki kamar yadda ake yi wa ma’aikatan gwamnati.

Mai magana da yawun hukumar zaben kasar ya bayyana cewa tsananin aiki ne ya kashe ma’aikatan zabe 272.

Hukumar zaben kasar dai na da niyyar biyan diyya ga iyalen wadanda abin ya shafa kusan dalar Amurka 2,500 ga duk iyalin ma’aikaci daya, kwatankwacin albashin shekara daya kenan na ma’aikacin kasar idan aka yi amfani da ma fi karancin albashi.

Jama’a da dama sun bayyana cewa gwamnatin kasar bata yi hikima ba wajen hada zabukan kasar wuri guda inda hakan ya jawo matsaloli.

Shugaban kasar ta Indonisiya Joko Widodo da kuma abokin hamayyarsa Prabowo Subianto, tuni kowane daga cikinsu ke ikirarin lashe zaben sai dai alamu na nuna cewa kamar Mista Widodo ne kan gaba.

Ana sa ran hukumar zaben kasar za ta kammala kirga kuri’un zaben kuma ta bayyana wanda ya lashen zaben a ranar 22 ga watan Mayu.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...