Iran na tsaka mai wuya bayan harbo jirgin Yukren | BBC Hausa

0
Jirgin ya fadi jim kadan bayan ya bar tashar jirgin saman Tehran kuma ya kone 'kurumus dauke da mutun 176

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Jirgin ya fadi jim kadan bayan ya bar tashar jirgin saman Tehran kuma ya kone ‘kurumus dauke da mutun 176

Iran na ci gaba da fuskantar suka daga kasashe bayan da amsa cewa ita ce ta kakkabo jirgin fasinjan Ukraine.

Jirgin ya fadi jim kadan bayan ya bar tashar jirgin saman Tehran kuma ya kone ‘kurumus dauke da mutun 176.

To sai dai an zargi Iran da harbo jirgin, ganin cewa faduwarsa ya zo dai-dai da lokacin da gwamnati a Tehran ta kaddamar da hare-hare kan sansanonin Amurka da ke Ira’ki.

Hakan ya biyo bayan kisan kwamandanta Qassem Soleimani da Amurka ta yi.

Da farko Iran ta musanta zargin, to amma ranar Asabar ta amsa cewa ita ta kakkabo jirgin kirar Boeing PS752 amma ‘bisa kuskure’.

Hakan ya sa wasu shugabannin ‘kasashe su ka fara kira da a dauki ‘kwa’kkwaran mataki kan Iran, kuma a gudanar da cikakken binciken ‘kasa da ‘kasa don gano gaskiyar yadda lamarin ya faru.

Shugabannin Yukren da Kanada su ne a ka fi jin muryoyinsu, kuma mafi yawan wadanda hatsarin jirgin ya shafa yan ‘kasashensu ne.

An tabbatar da cewa 57 daga cikin mutanen 176 ‘yan Kanada ne.

Image caption

An tabbatar da cewa 57 daga cikin mutanen 176 ‘yan Kanada ne

Shi ma Firanministan Burtaniya Boris Johnson ya bayyana daukar alhakin kai harin da Iran ta yi wani babban mataki ne na gano yadda hatsarin ya faru.

An gudanar da zanga-zanga ranar Asabar don nuna adawa da matakin gwamnati na daukar alhakin kai harin.

Ana kuma ci gaba da zaman makoki da nuna alhinin rashin mamatan.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ana kuma ci gaba da zaman makoki a Tehran da Toronto

A yanzu Shugaba Volodomyr Zelensky na Yukren na da jerin bukatu daga Iran kamar haka ;

  • Iran ta gurfanar da wadanda ke da alhakin kai wannan hari a gaban kotu
  • Dawo da wadanda suka mutu ‘kasashensu
  • Biyan diyya ga iyalan mamatan
  • Ba wa ma su bincike daga Yukren cikakkar damar shiga ‘kasar Iran din don gudanar da bincike.
  • Iran ta kuma ba da ha’kuri ta hanyar diflomasiyya

To amma masana na ganin Amurka ce ummul-haba’isin faruwar hatsarin, la’akari da cewa ita ta kunna wutar rikicin da ya yi sanadiyyar harbo wannan jirgi a ranar Larabar da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here