Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, a ranar Talata.
Yahaya wanda aka zaba a matsayin gwamnan jihar a shekarar 2019, ya sake lashe zabensa a karo na biyu a babban zaben watan Fabrairun 2023.
Zai karbi mukamin ne daga hannun shugaban kungiyar mai barin gado, Simon Lalong, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Filato.
An zabi Lalong a matsayin shugaban ƙungiyar ne a 2019.
