Hukumar USAID Za Ta Tallafa wa Jihohin Najeriya 7

An gudanar da taron kaddamar da shirin hukumar USAID ta kasar Amurka mai tallafa wa kasashe, wanda wannan shirin zai mai da hankali ne kan batun tantance ayyuka, fayyace su da kuma tabbatar da ingncinsu a fannoni daban-daban a wasu zababbun jihohin Najeriya.
Jihohin da za su amfana daga shirin sun hada da Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Ebonyi, Gombe da kuma Sokoto.
An yi da taron ne a kebabben wurin gudanarwa na jihar Bauchi. Gwamnonin jihohi guda shida da za su amfana da shirin sun gabatar da jawabansu ta akwatin talabijin.
Har ila yau wakilan hukumomin gwamnatoci da kuma jakadar kasar Amurka a Najeriya Mary Berth, da kuma Ministan Kudin Najeriya, sun gabatar da jawabai ta hanyar da aka haska su ta akwatinan telebijin da ake gani kai tsaye.
A bayan kammala taron, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir, ya ce gwamnatin jihar Bauchi, ta na maraba da wannan shirin, da kuma fatan zai taimaka wajen ciyar da jihohin gaba, da tabbatar da cewa ana amfani da kudaden al’umma yadda ya kamata.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...