Hukumar NDLEA na neman Abba Kyari kan zarginsa da safarar miyagun kwayoyi

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Kafin dakatar da shi kan alaka da dan damfara Hushpuppi da aka riga aka yankewa hukuncin damfara, Kyari shine Kwamandan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (IRT) a ofishin leken asiri na rundunar ‘yan sandan Najeriya.

A cewar hukumar ta NDLEA, ana neman sa ne a kan samun hannun sa a wani cinikin hodar iblis mai nauyin kilogiram 25.

Hukumar ta ce ta ayyana neman shi ne bayan duk kokarin da aka yi na ganin ya bayyana kansa biyo bayan gayyatarsa domin ayi masa tambayoyi ya ci tura.

Ya nuna takaicin halin da ake ciki inda wadanda ya kamata su goyi bayan kokarin da ake yi a halin yanzu na dakile bala’in fataucin miyagun kwayoyi sai kuma su da kansu, su shige ciki hanu dumu-dumi.

“Babu wata hanya mafi kyau da za mu fara wannan taron manema labarai da ya wuce tunatar da mu game da girman matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya da kuma wajibcin dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su taka rawar gani wajen dakile illolin miyagun kwayoyi,” in ji Mr. Babafemi yau Litinin.

Mr. Babafemi ya ce gaba da cewa, “Tun ma kafin a fitar da sakamakon binciken da aka yi a shekarar 2018 na amfani da muggan kwayoyi da lafiya, matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya na kara ta’azzara.

“Kuma a cikin watanni 12 kacal, hatta ’yan Najeriya da suka fi kowa son rai a yanzu sun yarda cewa da gaske kasar nan na cikin wani mawuyacin hali na miyagun kwayoyi, don haka ya yaba da irin namijin kokarin da jami’an NDLEA suke yi.

“Sai dai abin takaicin shi ne, wasu jami’an tsaro da ya kamata su kasance abokan hadin gwiwa wajen gudanar da aikin shugaban kasa su ne kan gaba wajen karya doka, yayin da suke taimakawa da safarar miyagun kwayoyi a kasar nan.

“A yau, an tilasta mana mu bayyana daya daga cikin irin wadannan jami’an tsaro da ake nema ruwa a jallo wato DCP Abba Kyari da aka dakatar, wanda shi ne kwamandan da ke ba da amsar bayanan sirri (IRT) a ofishin hukumar leken asiri ta rundunar ‘yan sandan Najeriya.

“Tare da bayanan sirrin da ke hannunmu, Hukumar ta yi imanin cewa DCP Kyari mamba ne na kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi da ke gudanar da haramtattun kwayoyi a Brazil-Ethiopia-Nigeria, kuma ana bukatar ya amsa tambayoyin da suka taso a cikin shari’ar miyagun kwayoyi da ke gudana wanda shi ne babban da ke kan gaba. Rashin shi ya bada hadin kai ya tilasta wa Hukuma wannan taron manema labarai.”

More News

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...