Hukumar Hisba A Kano Ta Kama Mota Dauke Da Kwalaben Giya 24000

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kama wata babbar mota dake dauke da kwalaben giya 24000 da kuma sauran nau’ikan giya.

Hukumar ta samu nasarar kama motar ne akan titin Zaria Road tare da wasu mutane biyu da kuma direban motar.

Darakta Janar na hukumar, Alhaji Abba Sufi shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na hukumar, Lawan Ibrahim Fagge.

Sanarwar ta ce an samu nasarar kama motar ne da tsakar dare akan titin na Zaria lokacin da mutanen suke kokarin fasa kaurinta ya zuwa birnin.

More from this stream

Recomended