Hukuma ta sake kama rikakken mai satar mutanen nan

Yanzu haka masana da kwararru a Najeriya sun yaba wa ‘yan sanda a kan namijin kokari da suka yi wurin zakulo mutumin, suna cewa wannan na nuna lalle fa ‘yan sandan Najeriya jajirtatttu ne.

Masanin Halayyar bil’adama da harkar tsaro, Farfesa Mohammed Tukur Baba ya ce wannan na nuna irin sabon babi da ‘yan sandan suka bude a sha’anin tsaro, duba da irin bajintar da suke ta nunawa da ba ayi tsammani ba, a don haka matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta ba wai ya gagari ‘yan sanda ba ne.

Farfesa Baba ya kara da cewa matakai da suke bi su kamo irin wadannan manyan yan ta’adda ya nuna cewa in sun dukufa kuma suka samu goyon bayan jama’a to fa lalle ‘yan sandan zasu magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Kamo irin wannan babban dan ta’addan inji masanin ka iya aikewa da sako ga duk masu son tafka aika aika, don hakan ya fara bada tsoro cewa lalle komai nisan jifa kasa zai fado, don kuwa dan sandan Najeriya ba kanwan lasa bane.

Lauyan nan mai fafutuka Barrister Yakubu Sale Bawa yace shi tuni yana da kwarin gwiwar lalle ‘yan sandan zasu sake cafke shi Wadumen, duba da cewar lalle ‘yan sandan Najeriya in zasu yi aiki zasu yi, kuma cafke wannan Wadumen zai fito da dalla dallan me ya faru.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...