Hotunan yadda annobar coronavirus ta sauya rayuwa a Birtaniya | BBC Hausa

Firai ministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa a shirye gwamnatin kasar take ta kara sanya matakai masu tsauri domin dakile yaduwar annobar coronavirus idan mutanen kasar ba su bi shawarar da aka basu ba ta bayar da tazara tsakaninsu.

A ranar Litinin, wurare da dama a tsakiyar birnin Landan babu hada-hada rjama'a kamar yadda aka saba

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A ranar Litinin, wurare da dama a tsakiyar birnin Landan babu hada-hadar jama’a kamar yadda aka saba

Duk da haka wasu jiragen kasa na karkashin kasa a Landan din na cike makil da mutane a safiyar ranar.

Hakkin mallakar hoto
PA Media

Image caption

Duk da haka, wasu jiragen kasa na karkashin kasa a Landan din na cike makil da mutane a safiyar ranar.

Masu tafiya da kafa kenan ke bi ta saman Gadar Landan, a da wurin na cike da mutane kowa na sauri domin tafiya hidimomi

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Masu tafiya da kafa kenan ke bi ta saman Gadar Landan, wurin da kafin yaduwar annobar na cike da mutane kowa na sauri domin tafiya hidimomi

Dandalin Trafalgar da rana shi ma babu jama'a kamar yadda aka saba

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dandalin Trafalgar da rana shi ma babu jama’a kamar yadda aka saba

BT Tower kenan, wata hasumiya da ke a Landan dauke da rubutu a can sama inda ake cewa a yi kokari a kare kai cikin irin wannan lokaci

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

BT Tower kenan, wata hasumiya da ke a Birtaniya dauke da rubutu a can sama inda ake cewa a yi kokari a kare kai cikin irin wannan lokaci

Tuni aka umarci mutanen Birtaniya da su killace kansu a gidaje kuma su kiyayi taron jama'a. An rage amfani da motocin haya a birane da dama a matsayin matakai na dakile yaduwar wannan cuta.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Tuni aka umarci mutanen Birtaniya da su killace kansu a gidaje kuma su kiyayi taron jama’a. An rage amfani da motocin haya a birane da dama a matsayin matakai na dakile yaduwar wannan cuta.

Wasu masu sayen kayayyaki kenan ke bada tazara tsakaninsu a daidai lokacin da suke kan layin shiga wani kanti

Hakkin mallakar hoto
PA Media

Image caption

Wasu masu sayen kayayyaki kenan ke bada tazara tsakaninsu a daidai lokacin da suke kan layin shiga wani kanti.

Birnin Leeds city na Ingila ya kulle dukkan wuraren wasan yara

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Birnin Leeds city na Ingila ya kulle dukkan wuraren wasan yara.

Wani wurin wasan yara da akarufe saboda coronavirus

Hakkin mallakar hoto
PA Media

Image caption

Wani wurin wasan yara da aka rufe saboda coronavirus

Wasu dawaki kenan ke sukuwa a birnin Newmarket biyo bayan sanarwar da aka yi kan dakatar da duk wani wasa na sukuwar dawaki a Birtaniya har zuwa karshen watan Afrailu.

Hakkin mallakar hoto
PA Media

Image caption

Wasu dawaki kenan ke sukuwa a birnin Newmarket biyo bayan sanarwar da aka yi kan dakatar da duk wani wasa na sukuwar dawaki a Birtaniya har zuwa karshen watan Afrailu.

All photographs subject to copyright.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...