Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar ya ƙaru zuwa mutane 15.
A ranar Laraba ne aka tabbatar da mutuwar mutum guda a yayin da wasu 24 suka jikkata bayan da wani matashi ya watsa fetur ya kuma cinna musu wuta.
Abdullahi Haruna Kiyawa mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce matashin da ake zargi da cinna wutar mai suna, Shafi’u Abubakar ya ce ya yi haka ne saboda rikicin gado shi da danginsa.
A ranar Alhamis mai magana da yawun rundunar ya ce mutanen da suka mutu sun ƙaru daga 1 daga ɗaya ya zuwa 6.
Sai dai kwamishinan ƴan sandan jihar, Usaini Gumel a ranar Juma’a ya ce ƙarin wasu mutanen sun mutu lokacin da suke samun kulawar likitoci a Asibitin Murtala dake Kano.