Hotunan wuraren bude ido na Saudiyya da za ku iya ziyarta | BBC Hausa

Ruins of the ancient city of Mada'in Saleh

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A karon farko a Saudiyya, kasar za ta bude kofofinta ga masu yawon bude ido daga kasashe 49 domin kai ziyara.

Kafin daukar wannan mataki, ana bayar da takardar biza ne kawai ga ma’aikata, da wadanda za su shiga kasar domin kasuwanci da kuma masu zuwa Umarah ko Hajji domin kai ziyara a Makka ko Madina.

Kasar ta kuma sha alwashin saukaka wa ta bangaren tsaurara wa mata kan irin kayayyakin da za su sa, kuma kasar za ta bar mata su iya shiga kasar ba lallai sai da muharrami ba.

Wannan na cikin sabbin tsare-tsare na kokarin kara habbaka tattalin arzikin kasar domin rage dogaron tattalin arzikin kasar kan man fetur – kuma wannan dama ce ga kasar na wanke kanta kan zarge-zargen da ake yi mata na take hakkin bil adama, ciki harda batun kashe dan jaridar nan Jamal Kashoggi.

Amma duk da haka, dole ne mata su yi shiga ta mutunci. Kuma wadanda ba musulmai ba, ba za a basu damar kai ziyara biranen Makka da Madina ba.

To me masu zuwa Saudiyya yawon bude ido za su je gani?

Ramin Al Wahbah

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

A cikin tsakiyar sahara, akwai wani rami mai tsawon kilomita 250 daga garin Ta’if mai suna Al Wahbah, wanda ya samo asali ne daga aman dutse.

Al Wahbah ya yi suna sakamakon yadda masu tattaki ke gasar tafiya a wurin. Ramin Al Wahbah na da zurfin kafa 820.

Jajirtattun masu tattaki na daukar kusan sa’o’i biyu zuwa uku kafin su je har kasan ramin kuma su dawo sama.

Wasu da basu son aikin wahala sosai, na zuwa wurin ne domin yada zango har su kwana domin hutawa.

Garin Mada’in Saleh

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mada’in Saleh shi ne gari na biyu mafi girma na kabilar Nabatean, wadanda wasu mutane ne da suka zauna a tsohuwar kasar Larabawa da kuma kwarin Jordan wanda daga baya Romawa suka mamaye wurin.

A halin yanzu, ana kai ziyara wata makekiyar makabarta mai kaburbura 130 da kuma wuraren bautar gumaka kafin zuwan musulunci da kuma wasu gidajen kasa.

Hukumar Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana Mada’in Saleh a matsayin wurin tarihi na duniya a 2008.

Tsohon birnin Jiddah da kuma kofar shiga Makkah

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wani wuri da Hukumar Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya da ta ayyana a matsayin wurin tarihi na duniya ita ce Kofar Makkah, wacce ke a tsohon garin Jiddah mai tarihi.

A karni na bakwai, an kafa Jiddah a matsayin tashar ruwa ta Tekun Indiya ga masu kasuwanci, da kuma ga Musulmai masu zuwa sauke farali da suka shigo ta ruwa da niyyar zuwa Makkah.

Ginin tarihi na Masmak

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ginin Maskmak da ke a birnin Riyadh an gina shi ne a 1864 – amma wurin ya yi suna ne bayan abin da ya faru shekaru 37.

A 1902, bayan an kori sarki Abdulaziz bin Abdul Rahman bin Faisal Al Saud, ya koma garinsa na asali wato Riyadh inda ya kwace ginin.

A lokacin da yake zaune a Masmak, ya je yaki inda ya yaki garuruwan larabawa, wanda bayan nan ne ya hada kan garuruwan inda suka zama abin da ake kira ”Kingdom of Saudi Arabia.”

Marmaron Sarki Fahad

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Marmaron Sarki Fahad shi ne Marmaro da yafi ko wane tsawo a duniya.

An bayyana cewa marmaron wanda Sarki Fahad ne ya gina shi kan iya harba ruwa tsawon kafa 853 – duk da cewa wasu sun bayyana cewa yana kai har kafa 1000.

Da dare, sama da fitulu 500 ne ke haskaka marmaron.

Umluj- ko kuma Maldives din Saudiyya

Hakkin mallakar hoto
Tharik Hussein

Wurin shakatawa na bakin ruwan da ke Umluj – wanda ake kira da Maldives ta Saudiyya, ganin cewa yanayin wurin na kama da kasar Maldives shi yasa ake wa wurin wannan lakabin.

Wurin na gabar tekun Bahar Maliya.

Zane a duwatsun Jubbah da Shuwaymis

Hakkin mallakar hoto
Tharik Hussein

Kamar yadda Hukumar Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, a zamanin da akwai Tafki kusa da wadannan duwatsun, wanda hakan yasa mutane da dabobbi suke taruwa kusa da su.

Mutanen da suka zauna a wurin sun yi zane a jikin duwatsun inda suka zana dabbobi da kuma yin wasu rubuce-rubuce.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...