Connect with us

Hausa

Hotunan da suka ci gasar kyawawan hotuna ta duniya | BBC Hausa

Published

on

Wani hoto da aka dauka na kauyen Upernavik inda ake kiwon kifi a tsibirin yammacin Greenland ya baiwa mai daukar hoto Weimin Chu damar lashe kyautar gasar kyawawan hotuna da matafiya ke dauka ta National Geographic Travel Photo Contest ta bana.

An snow-covered view of a street in the fishing village Upernavik in Greenland

Hakkin mallakar hoto
Weimin Chu

Mai daukar hoton ya shafe shekaru yana ziyara ne a Greenland kafin yanke shawarar ya dauki hotunan yadda jama’ar tsibirin ke rayuwa, inda ya fara da kauyen Upernavik.

Mista Chu ya tuna lokacin da ya isa yankin: “Kankara kawai nake gani ta mamaye dukkan tsibirin a lokacin da jirginmu ke sauka.

“Kyawun wurin ya kai matuka fiye da yadda nake tunani. Na yi mamaki sosai.”

Akwai kimanin mutum 1,000 da ke zaune a Upernavik, wanda shi ne kauye na 13 a kasar. Ya shafe kwana shida yana neman hotuna kafin ya ci karo da tawagar wasu iyali da ke tafiya a kusa da wata fitilar kan titi.

An zabi hoton Mista Chu a matsayin wanda ya ci gasar a bangaren hotunan da aka dauka a birane.

Ga sauran wadanda suka samu nasara da kuma bayani kan hotunansu:

Presentational grey line

Na biyu – birane – daga Jassen Todorov

Aerial view of a plane coming in to land on a runway

Hakkin mallakar hoto
Jassen Todorov

“Akwai titunan saukar jiragen sama hudu a filin jirgn sama na San Francisco da ke Amurka. Na samu damar daukar hoton filin da kuma zagaya shi a jirgin sama.

“Sai dai an yi iska sosai a ranar wacce ke gudun mil 35-45 a duk sa’a, wanda hakan ya sa jirgin ya ringa yin gargada, ya kuma sa na sha wahala wurin kula da jirgin a lokacin da ake daukar hoton.” – In ji Jassen Todorov.

Presentational grey line

Na uku birane: Titunan birnin Dhaka, daga Sandipani Chattopadhyay

People praying on the street in Dhaka

Hakkin mallakar hoto
Sandipani Chattopadhyay

“Jama’a kan yi sallah a kan titi a birnin Dhaka, na Bangladesh a lokacin bikin addini na Ijtema. Bishwa Ijtema na daya daga cikin manyan bukukuwan addinin Musulunci da ake yi duk shekara a Dhaka, kuma miliyoyin Musulmai ne ke ziyara a lokacin.

“Wurin da aka ware domin sallah ba ya isar mutanen da ke halartar bikin, a don haka mutane da dama ke zuwa [Tongi], babban titin birnin domin yin sallah. Ana dakatar da dukkan ababan sufuri a lokacin.” – Sandipani Chattopadhyay

Presentational grey line

Na daya a banagaren hotunan mutane, daga Huaifeng Li

Actors put make-up on before a performance

Hakkin mallakar hoto
Huaifeng Li

“‘Yan fim na shirin yin wasa a wani dandali a yankin Licheng na kasar China. Na shafe kwana guda tare da ‘yan fim daga lokacin da suke kwalliya har zuwa dandali”.

“A dutsen Loess na China, jama’ar yankin sun haka wani katon rami domin samar da wani kogo domin zama, [wanda aka fi sani da yaodongs] sannan su yi amfani da hanyoyin rage zafi domin kauce wa yanayin sanyi.” – Huaifeng Li.

Presentational grey line

Na biyu a banagaren hotunan mutane, daga Yoshiki Fujiwara

A man performs tai chi in front of a block of flats

Hakkin mallakar hoto
Yoshiki Fujiwara

“An dauki wannan hoton ne a wani wurin shakatawa a Hong Kong. Lokacin da na kai ziyara da yamma, a cike wurin yake da matasa suna daukar hotuna da kuma yin kwallon kwando.

“Amma lokacin da na koma wurin da maraice, sai na ga wurin daban. An ware wurin ne domin zaman jama’a da safe. Na ci karo da wani dattijo yana motsa jiki irin na Taichi.” – Yoshiki Fujiwara

Presentational grey line

Presentational grey line

Na daya a banagaren hotunan halittu, dagaTamara Blazquez Haik

A close shot of a vulture flying

Hakkin mallakar hoto
Tamara Blazquez Haik

“Wata ungulu ce da aka dauko hotonta lokacin da take shawagi a sararin samaniyar gandun dajin Monfragüe National Park a kasar Spaniya.

“Me zai sa wani ya ce ungulu na kawo bala’i? Ungulu tana da muhimmanci ga muhalli,” in ji Tamara Blazquez Haik.

Presentational grey line

Na biyu a banagaren hotunan halittudaga Danny Sepkowski

A large wave is seen before it breaks

Hakkin mallakar hoto
Danny Sepkowski

“Me zai faru kafin igiyar ta tsinke? Wannan ita ce tambaya da na sanya a gabana a bara. A wannan rana, na kudiri aniyar daukar hoton faduwar rana a garin Oahu a jihar Hawaii a kasar Amurka,” in ji Danny Sepkowski.

Presentational grey line

Na ukua banagaren hotunan halittu, daga Scott Portelli

A black and white photo of a dolphin swimming through water

Hakkin mallakar hoto
Scott Portelli

“Wannan wani jinsin kifi ne wanda yake tafiya a ayari a gabar tekun Kaikoura a kasar New Zealand don neman abinci, ” In ji Scott Portelli.

Presentational grey line

Hoton halittun da aka ambato wanda Jonas Schafer ya dauka

A herd of ibexes are seen on a mountain ridge

Hakkin mallakar hoto
Jonas Schafer

Wadannan dabbobin an dauki hotonsu ne a kasar Switzerland yayin da suke kokarin tsallake wata gaba a tafkin Brienz.

Hotuna daga National Geographic Travel Photo Contest 2019.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Arewa

Najeriya ta yi fatali da bukatar makwabtan kasashe na bude iyakokinta

Published

on

Bisa dukan alamu, Ministocin Kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin da suka bukaci bude iyakokin Najeriya da aka rufe tun watan Agustan bana cikin gaggawa, sun fice cikin fushi daga taron da Wakilan Gwamnatocin Kasashen da ke Makwabtaka da Najeriya suka yi a Abuja akan halin da kasashen suka tsinci kansu tun bayan rufe iyakokin Najeriya,domin kuwa Ministan Kula da harkokin wajen Najeriya Geofrey Onyeama ya karanata wa Manema Labarai Jawabin bayan taron daga shi sai ‘yan’uwansa na cikin gida.

Kasar Nijar da ke Makwabtaka da Najeriya ta bangaren Arewa ta bayana cewa rufe iyakokin na kasa, ya jawo mata asarar makudan kudade da yawan su ya kai CEFA miliyan 40, kimanin dalar Amurka miliyan 67, Kwatankwacin fiye da Naira miliyan 24 a Kudin Najeriya.

Ministan Kula da Harkokin Cikin gida na Nijar Mohammed Bazoum da ya fice kafin a gama taron ya ce Najeriya ta dauki mataki mai zafi na rufe kan iyakokin ta da Kasashen uku ne a bisa abinda ta kira matsalolin da ta ke fuskanta na fasa kwabri, su ma kansu Nijar wanan matsala tana shafan su, shi ya sa a yau suka taru domin lalubo mafita wacce ba za ta cutar da kowace kasa ba.Saboda matsalar fasa kwari ta addabi kasashen da ke makwabtaka da Najeriyan ne duka.

To saidai Karamin Ministan Hulda da Kasashen waje na Najeriya Ambasada Zubairu Dada ya bayyana wa manema labarai cewa wuni muhimmin mataki da taron ya dauka shi ne na nada wani komiti na musamman da ke dauke da jami’an Kwastan, da na jami’an Shige da Fice,da na Hukumomin tsaron kasashen uku, da zai yi rangadi da sintiri a kan iyakokin kasashen sannan ya bada rahoto da Najeriya za ta duba yiwuwar bude iyakokin ta.

Amma ga mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum Aminu Jumare yana ganin ba a bi dokokin Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma wajen rufe iyakokin Najeriya ba.

Nan da makonni biyu na gaba Komitin Kula da harkokin tsaro za ta sake wani taro a Abuja babban Birnin Najeriya.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Messi zai buga wa Argentina kwallo ranar Juma’a

Published

on

Lionel Messi

Hakkin mallakar hoto
Quality Sport Images

Image caption

Har ila yau Argentina za ta kara da Uruguay a birnin Tel Aviv a ranar Litinin

Lionel Messi na cikin tawagar da za ta wakilci kasar Argentina a wasan sada zumunci da za ta fafata da Brazil a kasar Saudiyya ranar Juma’a.

Wannan ne karon farko da dan wasan zai fito a wasa irin wannan tun bayan korarsa daga filin wasa a gasar Copa America a fafatawar kasarsa da Chile cikin watan Yuli.

An dakatar da dan wasan na Barcelona, mai shekara 32, har tsawon watanni uku bayan da ya ayyana cewa ana magudi a gasar.

Hakazalika dan wasan Aston Villa Douglas Luiz a karon farko na cikin tawagar da za ta wakilci Brazil a wasan.

Wannan shi ne karo na farko da kasashen biyu biyu za su yi wasa tun bayan da Brazil ta doke Argentina da ci 2-0 a wasan kusa da na karshe a gasar Copa America.

Brazil ta kasa cin nasara a wasanni hudu tun lokacin, da ta sha kaye a hannun Peru da ci 1-0 a watan Satumba, yayin da Argentina ta samu nasara a wasanni hudu a lokacin da aka dakatar da Messi, inda ta doke Ecuador 6-1 a watan da ya gabata.

Har ila yau Argentina za ta kara da Uruguay a birnin Tel Aviv a ranar Litinin, amma ana ganin za a iya dakatar da wasan saboda rikicin da ke faruwa a Isra’ila.

Ita kuwa Brazil za ta kara da Koriya ta Kudu a birnin Abu Dhabi ranar Talata, wanda zai kasance wasansu na karshe kafin fara wasannin share fagen shiga Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 da za fara a watan Maris.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Hotuna: Labarin addinin Yarsan da ba a san shi ba sosai | BBC Hausa

Published

on

Yarsani Soltan

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Wurin bautar na yankin Kermanshah da ke yammacin Iran. Iddinin Yarsan ya samo asali ne tun karni na 14th ko 15th Century, ya na kuma kamanceceniya da mazhabar Shi’a. Addinin na da littafi mai suna Kalam-e Saranjam, da aka dora bisa koyarwar Sultan Sahak.

Addinin Yarsan na daga cikin tsofaffin addinai a Gabas Ta Tsakiya

Ana kiran addinin Ahl-e Haqq da harshen Larabci, ma’ana mutane masu gaskiya.

An yi kiyasin akalla akwai mabiya addinin miliyan uku a kasar Iran, wadanda yawanci ke zaune a yammacin kasar inda Kurdawa ke da rinjaye. Yayin da wasu mabiya 120,000 zuwa 150,000 ke kasar Iraqi, inda aka fi kiran su da suna Kaka’i.

Wata mai bincike mai suna Behnaz Hosseini, daga jami’ar Oxford wadda ke nazari kan tsirarun addinai a kasashen Iran da Iraqi, a kwanakin baya, ta shafe lokaci mai tsaho cikin mabiya addinin Yarsani a lokacin azumin kwana uku da suke yi.

Yarsani tanbur

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Mabiya addinin Yarsani su na amfani da goge a lokutan bukukuwan addini da suke kira”tanbur” da rera wasu baitoci da kalamai da ake kira “kalam”

Yarsani Jamkhaneh

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Mabiya addinin Yarsani na taruwa a kowanne wata a wani wuri da ake kira “jamkhaneh”. Ana kiran taron da “jam”.Duk wanda ya shiga zaman na jamkhaneh dole ne ya bi wasu ka’idoji, ciki har da sanya wata hula ta musamman. Sannan su na yin da’ira su na kallon wani wuri na musamman da aka kebe a cikin jamkhaneh

Yarsani Khavankar

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Yarsani su na yin azumi uku a watan Aban na jerin watannin da kasar Iran ke amfani da su, wanda ya ke farawa daga watan Oktoba zuwa Nuwamba.

Yarsani Khavankar

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

A kowanne dare, al’ummomin da ke bin addinin Yarsani su na gudanar da zaman addu’ar jam’i a lokacin azumi da suke shan ruwa idan rana ta fadi

Yarsani vow

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Ana gasa biredi da tafasasshen ruwan nama ko farfesu a lokacin shan ruwa

Yarsani pomegranate

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hossein

Image caption

‘Ya’yan itatuwa na ruman na daya daga cikin kayan marmari masu muhimmanci ga mabiya addinin Yarsani musamman lokacin bukukuwa

Yarsani moustache

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Gashin baki wata alama ce ta daukaka da girmamawa ga al’umar Yarsani, maza na tara gashin baki ba tare da askewa ko ragewa ba

Yarsani Jam ceremony in Iran

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Sai dai kundin tsarin mulkin Iran bai amince da mabiya Yarsani marasa rinjaye ba kamar mabiya addinin kirista da Yahudawa ko Zoroastrians. A maimakon haka, gwamnati kan dauki ‘yan Yarsani a matsayin mabiya mazhabar Shi’a da ke bin tafarkin Sufaye. Wasu daga cikin malaman Shi’a a Iran na kallon wadannan mutane da wadanda ba su yi imani da mazhabarsu ba

Yarsani Tirikardan

Hakkin mallakar hoto
Behnaz Hosseini

Image caption

Yawancin mutanen sun shaida wa Majalisar Dinkin Duniya shekarar 2018 sun gagara yi wa ‘ya’yansu rijistar haihuwa, saboda an haramta musu yin haka ba sa iya zaman makoki idan dayansu ya mutu kamar yadda addini ya tanada, sannan ba a ba su damar wallafa littafan addininsu ba , sannan ana hukunta su da cin zarafin addinin musulunci da kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW. Yayin da sojoji ke tilastawa wasu yanke gashin bakinsu

Wadannan hotunan mallakar Behnaz Hosseini ne.

Facebook Comments
Continue Reading

Trending

© Copyright 2019 - AREWANG Media Limited