Hazard ya yi ‘sallama’ da Chelsea; Bayern Munich na ‘son’ Dybala

Eden Hazard

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shahararren dan wasan Chelsea Eden Hazard ya yi hannunka mai sanda game da barin kungiyar bayan ya ci kwallo biyu a wasan karshe na Europa da suka casa Arsenal da ci 4-1.

An jima ana alakanta dan wasan da koma wa Real Madrid, kuma jim kadan bayan tashi daga wasan ya ce:

“Ina ganin na yi bai-bai ga magoya bayan Chelsea amma ka san a harkar kwallo komai ka iya faruwa. Ya kara da cewa “yana jiran kungiyoyin biyu” su daidaita, kamar yadda ya shaida wa BT Sport.

Bayern Munich

Bayern Munich ta kai tayin fan miliyan 80 domin daukar dan wasan gaban Juventus Paulo Dybala, kamar yadda jaridar Corriere dello Sport ce ta ruwaito.

Manchester United

Ashley Young kaftin din Man United mai shekara 33 ka iya hadewa da tsohon abokin wasansa a Wayne Rooney a kulob din DC United da ke Amurka, in ji Manchester Evening News.

An sanar da dan wasan gaban Man United Romelu Lukaku cewa zai iya barin kungiyar zuwa Inter Milan, a cewar jaridar Sun.

Paris St-Germain

PSG tana tattaunawa da Barcelona domin dauko dan wasa Ousmane Dembele mai shekara 22 a matsayin musaya tsakaninsa da Neymar, in ji rahoton RAC1 Sport.

Real Madrid

Dan wasan baya mai buga bangaren hagu a kungiyar Lyon kuma dan kasar Faransa Ferland Mendy, mai shekara 23, zai koma Real Madrid da taka leda, a cewar rahoton jaridar AS .

More News

Kotu ta bayar da belin Hadi Sirika da Ć´arsa

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da kuma wasu mutane uku kan...

Kotu Ta Hana PDP Cire Shugaban RiĆ™on Jam’iyar

Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta hana jam'iyar PDP dakatar da Umar Damagum daga matsayinsa na shugaban riƙon jam'iyar. Mai Shari'a  Peter Lifu shi...

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...