Harin Taliban ta kai ya asibiti ya kashe mutum 15 | BBC Hausa

Motocin da harin Taliban ya lalata a in Qalat, shalkwatar lardin Zabul province, Afghanistan a ranar 19 ga watan Satumba, 2019
Hakkin mallakar hoto
Reuters

Akalla mutum 15 sun mutu cikinsu har da likitoci da majinyata a harin da kungiyar Taliban ta kai wani asibiti a kudancin Afghanistan.

Likitoci da majinyata ne akasarin mutanen da suka mutu a harin da kungiyar ta kai a yankin Qalat da wata mota makare da ababen fashewa.

Wasu rarotanni sun bayyana cewa wasu mutum 15 sun mutu a wani harin sama da kungiyar IS ta kai a gabashin kasar.

Akalla fararen hula 473 ne aka kashe a rikice-rikicen kasar, kamar yadda BBC ta gano.

Binciken na BBC ya gano cewa fararen hular sun kai kimanin kashi daya bisa biyar na yawan mutanen da aka kashe a kasar a watan Agusta.

Abin da ya faru a asibitin?

Wani babban jami’i a ma’aikatar tsaron Afghanistan ya sheda wa Reuters cewa an tayar da wani babban bam ne da aka dauka a wata karamar mota kirar a-kori-kura a kusa da asibitin da ke Qalat.

Rahotanni sun bayyana cewa asibitin ne cibiyar kula da lafiya mafi girma a yankin Zabul.

Taliban ta ce ta kai harin ne a kan ofishin tara bayanan sirri na kasar da ke makwabtaka da asibitin.

Ba a samu hakikanin adadin mutanen da harin na ranar Alhamis din ya rutsa da su ba.

Shugaban yankin ya ce an gano gagawarwaki kusan 20 da kuma karin wasu mutum 100 da suka jikkata.

Shedun gani da ido sun ce sun ga ana ceto mata da kananan yara daga baraguzan gini.

“Abun na da ban tsoro” kamar yadda wani dalibin jami’a Atif Baloch ya sheda wa AFP.

Motocin agaji na ta jigilar daukar gawarwaki zuwa asibitoci a yankin Kandahar mai makwabtaka da yankin.

Taliban na ci gaba da kai hare-hare a kusan kullum, a yayin da zaben kasar na watan Oktoba ke kara matsowa. A ranar Talata, kungiyar ta kai wa shugaba Ashraf Ghani farmaki a lokacin da yake gab da yin jawabi a wurin ganmamin yakin neman zabensa, wanda ya yi sanadiyar mutwar mutum 26.

However, despite the Taliban attacks hitting the headlines, United Nations statistics have shown more civilians were killed by Afghan and US forces in the first half of 2019 than by insurgents.

Duk da hare-haren da Taliban ke kai wa yayin da wa’adin ke kara matsowa, alkalumun Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa mutanen da dakarun Amurka da na Afghanistan suka kashe a farkon 2019 sun fi yawan wadanda ‘yan tada kayar bayan suka kashe a tsawon lokacin.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...