Connect with us

Hausa

Hajj 2019: Amsar tambayoyinku kan ayyukan da suka shafi Hajji | BBC Hausa

Published

on

Hajj 2019

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wannan makala ce da ta amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko kan aikin Hajji. Mun yi bincike tare da jin ta bakin Masana kan muhimman abubuwan da suka shafi ayyukan Hajji.

Aikin Hajji, daya ne daga cikin shikashikan Musulunci biyar, da ake wajabta wa Musulmai masu hali su yi ko da sau daya ne a rayuwarsu.

Ana gudanar da aikin Hajji ne a kwanaki biyar wanda ake farawa daga 8 ga Zul Hajji zuwa 12 ko 13 ga watan.

A duk shekara sama da mutum miliyan biyu da rabi ne ke gudanar da aikin Hajji a Saudiyya, wanda shi ne taro mafi girma a duniya.

Hukumar alhazai ta Najeriya ta ce alhazan kasar sama da dubu arba’in ne suka isa Saudiyya domin ibadar.

Kwamishinan Gudanarwa na hukumar Abdullahi Modibbo Saleh ya shaida wa BBC cewa a bana kimanin ‘yan Najeriya 45,000 ne suka aikin Hajjin 2019 .

BBC Hausa ta yi nazari ta hanyar tattaunawa da Malamin Addini kan muhimman abubuwan da suka shafi aikin Hajji, da kuma Kakakin Hukumar Alhazzai ta Najeriya wadanda kuma suka yi kokarin amsa wasu tambayoyi da kuka aiko mana.

Banbamcin Farillai da wajiban ayyukan Hajji

Dakta Mansur Yalwa, Malamin addinin musulunci ne a Najeriya, wanda kuma cikin masu aikin hajjin na bana, ya ce Farillan aikin hajji guda hudu ne, akwai kuma ayyukan da suka wajaba ga mai niyyar aikin hajjin.

Farillan Hajji su ne wadanda idan ba a yi ba Hajjin mutum ya rushe, wato ma’ana hajjin bai yi ba – wajibi kuma za a yi diyya ta hanyar yanka.

Farillan sun kunshi Niyya da Dawafi da sa’ayi (Safa da Marwa) da kuma Arfa.

Ayyukan da ake kira Wajibai sun kunshi Kwanakin da ake yi a Mina da kwanan Muzdalifa da jifan Shaidan da kuma yin aski.

Mutum sai ya yi yanka idan bai yi daya daga cikinsu ayyuka wajibai ba.

Niyya – Mikati

Niyya kamar yadda Dakta Mansur ya fada tun da farko tana daga cikin Farillan Hajji.

Niyyar Hajji tana da iyaka inda ba a wuce wani wuri na daukar Niyya da ake kira Mikati. An fi son mutum ya zo Mikati ya dauki niyyar Hajji ko Umrah.

Malamin ya ce, Mikati wurare ne da Annabi SAW ya yanka wa al’umma na ko wane sashe na duniya inda za su dauki niyya.

“Hadisin Abdullahi bin Umar ya ruwaito Annabi SAW yana cewa – Wasu za su dauki niyya daga Juhfa da Zul-Hulaifa, wasu daga Yalamlam, wasu kuma daga Qarnul Manazil.”

Duk inda ka fito daga duniya ba zaka wuce daya daga cikinsu ba sai ka tsaya ka dauki niyya.

Duk mutanen da suka fara sauka a Madina, Musamman kamar yawancin Maniyyatan da ke fara zaman Madina, kafin isa Makkah to Mikatin da za su dauki niyyar Umrah da Hajji ana kiransa Zul-Hulaifa.

Mikatin yana nan kan hanyar Madina zuwa Makkah inda aka ware kuma aka tanadi wurin wanka domin maniyyata.

Amma Dokta Mansur ya ce wadanda ba za su samu zuwa Madina ba, wato wadanda aka ajiye a Jeddah, za su dauki niyya kafin su sauka daga jirgi saboda kafin Jeddah sun riga sun wuce mikati.

“Idan mutum ya wuce Mikatin shi bai yi niyya ba to yanka ya hau kansa,” in ji Dakta Mansur.

Ya ce asalin Mikatin mutanen Afirka yana wani wuri ne da ruwa ya mamaye wanda ake wucewa a cikin jirgi kafin sauka birnin Jeddah inda ba za a iya tsayawa ba.

Idan Maniyyaci ya riga ya isa birnin Jeddah to ya riga ya wuce inda mikatin yake.

A takaice ba a son a wuce Mikati ba tare da mutum ya yi Ihrami ba, wato wurin ne ake daukar niyyar Hajji ko Umrah.

Nau’in ayyukan Hajji

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu mahajjata sun dafa dakin Ka’aba, wanda ake kewaya wa sau bakwi yayin dawafi

Hajj Ifradi – Wannan da Hausa ana nufin kadaitawa, wato nau’in aikin Hajji ne da za a yi iri daya da niyya daya.

Mutum zai dauki niyyar zai yi Hajji ne kadai ba zai yi Umrah ba, domin Umrah ba farilla ba ce.

Dokta Mansur ya ce Maniyyaci zai dauko niyyarsa daga Mikati ta aikin hajji kadai.

Idan mutum ya sauka Makkah zai fara dawafin isowa. daga nan sai ya gudanar da sauran ayyukan Hajji. Tun ranar da mutum ya shigo zai ci gaba da ayyukansa har zuwa kammala aikin hajji.

Banbamcinsa da sauran nau’ukan aikin Hajji shi ne babu yanka amma sauran ana yanka.

Hajj Tamattu‘i – Shi ne a fara yin Umrah daga baya a yi aikin Hajji.

Hajj Tumattu, shi ne mafi yawanci wanda aka fi yi saboda saukinsa. Malam ya ce ana yin su ne daban-daban, wato aiki biyu da niyya biyu daban.

Mutum zai dauko haramar yin Umrah daga Mikati ba tare da daura niyyar yin aikin Hajji ba.

Kamar wadanda suka kammala zaman Madina, za su tsaya mikati a Zul-Hulaifa su saka harami.

Umrah kuma ta shafi gudanar da abubuwa uku da suka kunshi daura Niyya da Dawafi da sa’ayi (Safa da Marwa).

Bayan an gama sai mutum ya sa kayansa na gida ya zauna Makkah a masaukinsa ya huta har zuwa ranar 8 ga wata da za a fita a fara aikin Hajji.

A Hajj Tumattu’i, maniyyaci zai samu lada biyu na aikin Umurah da Hajji. Kuma ana yin yanka.

Idan mutum ya gama Umrah zai iya yin duk abin da aka hana shi, har saduwa da iyalinsa idan suna tare, a kwanakin da ke tsakanin Umrah da Hajji.

Hajji Kirani – Shi ne a gudanar da aikin Hajji tare da Umrah. Wato za a yi aiki biyu da niyya daya.

A Hajj Kirani, Malam ya ce maniyyaci zai dauki niyya ne daga Mikati cewa zai yi aikin Umrah da hajji a hade.

Yana isa Makka zai yi dawafin isowa sannan ya ci gaba da zama cikin haraminsa.

Idan aka fito aikin Hajji a ranar 8 ga wata ba sai ya sake daukar niyya ba.

Sai idan ya koma Makkah zai yi Dawafi wanda zai kasance matsayin na Umrah da Hajji, bayan kammala ayyukan Hajji, kamar zaman Minna da jifa.

Zai yi Sa’ayi na Hajji da Umrah kuma zai yi aski sannan zai yi yanka.

Malam ya ce Hajj Kirani, galibi mata ne suka fi yawan yinsa saboda matsalar jinin haila da suke yi.

Ya ce idan mace ta dauki niyyar Hajj Tumattu, sai haila ta zo – tana iya canza niyyar zuwa Kirani sai ta jira zuwa lokacin aikin Hajji.

“Za ta iya yin ayyukan Hajji ba ta da tsarki kamar kwanan Minna da Arfa da muzdalifa da jifa,” in ji Dr Mansur.

Haka kuma ya ce idan ta dawo Makkah za ta yi Dawafi na Umrah da Hajji – “kenan ta koma Kirani maimakon Tumattu’i da ta dauko niyya tun da farko.”

Aikin Hajji

Image caption

Mina nan ne ainihin wajen da alhazai ke tafiya a ranar 8 ga watan Zul Hijjah don gudanar da aikin Hajji inda su kan shafe tsawon kwana hudu zuwa biyar. Waje mai matukar girma da aka kafa tantuna don zaman alhazai.

Image caption

Tantunan Mina

Aikin Hajji baki dayansa wuni biyar ne, kuma ana fara wa ne daga 8 ga watan Dhul Hajji.

Amma Malam ya ce zuwa Mina domin shirin zuwa Arfa a ranar ba wajibi ba ne sunnah ce.

Ranar 9 ga wata ake hawan Arfa, sai dai a Arfa ba za a wuce ranar 9 ga wata ba. A ranar 10 kuma a yi Sallah.

Dukkanin wunin 11 da 12 da 13 ana yinsu ne a zaman Mina.

A filin Arfan ne ma’aiki, Annabi Muhammad (S.A.W) ya yi hudubarsa ta karshe kafin ya bar duniya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Filin arafah shi ne kololuwar wajen gabatar da ibadah a lokacin aikin Hajji. Wannan shi ne dutsen Rahma dake filin Arfah, amma a yanzu an fadada wajen ta yadda ‘yan wasu kasashen ma su kan zauna ne nesa sosai da dutsen saboda irin cikowar da ake yi.

A tsayuwar Arfa ana yin Sallar Azahar da La’asar duka ra’aka biyu. Ana addu’a da zikiri da ambaton Allah a yayin tsayuwar Arfa.

Sai bayan rana ta fadi a wuce Muzdalifa inda za a yi Magariba da kuma Issha, amma kasaru ra’aka biyu.

A Muzdalifa ake kwana cikin harami bayan tsayuwar Arfa, kuma ba a addu’a da karatun Qur’ani mai tsarki, mutum zai kwanta ne ya yi baccinsa zuwa da safe ya wuce zuwa jifa.

Jifa – Ranar Sallah

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wajen jifan Shaidan da aka fi sani da jamrah na daga cikin wuraren ibada masu muhimmanci lokacin aikin hajji.

A ranar Sallah ne ake yin jifan Jamrah da ake kira jifar Shedan. Kuma ayyuka kusan biyar ne ake yi masu muhimmaci a wannan ranar.

Jamratul Akabah- Wuraren jifa uku ne, amma a ranar sallah daya kawai ake jifa ta karshe. Duwatsu kanana guda bakwai da ba su wuce girman kwayar gyada ko wake ba ake jifa da su, in ji Dakta Mansur Yalwa

Za a iya tsinta tun daga Muzdalifa ko kuma a hanya. Bayan kammala jifa, akan kalli alkibla a yi addu’a. Daga nan sai a yi yanka da kuma aske gashin kai gaba daya, ko kuma saisaye.

Bayan mutum ya yi jifa ya yi yanka da aski, sai ya isa Makkah ya yi dawafi ya yi Safa da Marwa.

Mahajjaji zai cire harami ya je ya yi wanka ya sa kayansa na Sallah idan Tuma’attu’i yake.

A ranar 10 ga wata za a koma Mina a yi kwanakin Minna a ci gaba da zikiri.

Za a dinga zuwa jifa da rana a kwanakin 11 da 12. Daga kwana na 12 mutum zai iya komawa Makkah ko kuma ya sake kwana zuwa 13 ga wata.

Safa da Marwa

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wannan shi ne wajen Safa da Marwah inda ake so alhazai su yi sassarfa sau biyu daga Safa zuwa Marwa.

Babu banbamcin yadda ake sa’ayi a aikin Hajji da Umrah, haka ma yadda ake Dawafi.

Ana farawa ne a kan Safa a yi addu’a. Sai a tafi zuwa Marwa a matsayin turmi daya. Za a yi haka har sau bakwai.

Hakan na nufin za a fara a Safa a kare a Marwa.

Dutsen Safa da Marwa

kamar yadda Allah ya fada a Alkur’ani mai girma “Lallai ne Safa da Marwa suna daga wuraren ibadar Allah, to, wanda ya yi aikin Hajji a dakin ko kuwa ya yi Umra, to, babu laifi a kansa ya yi dawafi tsakaninsu. Kuma wanda ya kara yin wani aikin alheri to, lallai ne wadannan su ne shiryayyu.” Surah Bakara aya ta 158.

Dutsen Safa inda daga nan ake fara Sa’ayi yana da nisan kilomita 0.80 daga Dakin Ka’aba. Yayin da Dutsen Marwah yake da nisan mita 100 daga Dakin Ka’abah.

Nisan da ke tsakanin duwatsun biyu kuwa mita 450 ne.

Dawafin ban-kwana

Image caption

Dawafi a dakin ka’aba na daga abubuwan da ake so mai aikin hajji ya yawaita

Bayan kammala kwanakin Mina da kammala Sa’ayi da dawaful Ifada, mutum ya kammala aikin hajjin sa. Babu abinnda ya rage masa sai dawaful wada’i, wato dawafin ban-kwana da dakin Ka’abah.

Ana so aikin karshe da mutum zai yi a Makkah gabanin koma wa kasarsa, shi ne dawafi da nufin ban-kwana.

Amma gabanin dawafin, Dakta Mansur yace ana so mai aikin hajji ya ringa yawaita yin sallah a masallacin harami, wato Ka’abah, sannan lokaci zuwa lokaci, ya ringa yin dawafi a dakin.

Zaman Madina

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Maniyyata na zuwa Madina domin yin sallah a masallacin Manzon Allah da kuma ziyartar kabarinsa SAW

Mafi yawancin Maniyyata kan fara sauka birnin Madina domin Ibada a Masallacin Manzo SAW da kuma ziyarce-ziyarce.

Babbar ibadah da ake yi a Madina ita ce gudanar da sallah a masallacin Annabi SAW.

Manzo SAW ya ce sallah guda daya a cikin masallacinsa a Madina, ta fi falala sama da yin sallah a wani masallaci da lada 1,000 idan dai ba msallacin ka’aba ba ne, wanda sallah a cikinsa take da lada dubu dari sama da sauran masallatai.

Wannan falalar ce mutane suke kwadaituwa da ita, saboda muhimmacin samun sallah a masallacin Annabi wanda ya fi komai muhimmacin a garin Madina.

Ana ziyarce ziyarce a Madina, kamar makwancin Manzo SAW a Masallacinsa da kuma sahabbansa a yi masu sallama.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dakin da ake binne Manzon Allah SAW da Sahabbansa Sayyidina Abubakar da Umar RA.

Dokta Mansur ya ce, ana ziyartar masallacin Quba, wanda Annabi SAW ya fara aza tubalinsa – Annabi ya ce duk wanda ya yi alwala daga gida ko masauki ya je masallacin Quba ya yi sallah zai samu lada kwatantakwacin wanda ya yi Umrah.

Malamin ya ce, ana ziyartar makabartar Baki’a da ke gefen Masallacin Annabi. Sannan kuma ana ziyartar inda aka binne sahabbai 70 da aka kashe a yakin Uhudu da suka hada da Sayyidina Hamza RA.

Ziyartar Makabatar Baki’a sunnah ce wato makabartar da aka binne Sahabbai sama da 10,000. Ana kuma ziyarartar wuraren tarihi, irin Masallaci mai alkibla biyu.

Image caption

Jama’a suna zama domin jiran yin sallah masallacin Madina

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Rashida da Ilhan: Musulman da suka ‘tsone wa Trump da Isra’ila ido’ | BBC Hausa

Published

on

Congresswomen Ilhan Omar (left) and Rashida Tlaib

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yar majalisar wakilan Amurka Ilhan Omar (daga hagu) da kuma Rashida Tlaib

Rashida Tlaib da Ilhan Omar sun kafa tarihi a watan Nuwamban 2018 lokacin da suka zamo Musulmai mata na farko da suka lashe kujerun majalisar wakilai a tarihin Amurka.

Duka matan dai mambobi ne na jam’iyyar Demokurat kuma sun dace da irin siyasar kawo sauyi da jam’iyyar ke cewa tana yi.

Sun nuna goyon baya ga dokokin ‘yancin dan’adam, ciki har da na zubar da ciki da kuma goyon bayan masu zuwa ci-rani.

Sai dai akwai wani abu daya da ya sa suka raba-gari da sauran ‘ya’yan jam’iyyar ta Demokurat da ma na Republican: Isra’ila.

Kauracewa Isra’ila

Duka matan biyu na matukar sukar yadda Isra’ila take muzguna wa Falasdinawa, kuma su kadai ne ‘yan majalisar da suka fito karara suka nuna goyon baya ga kungiyar Falasdinawan da ke jagorantar kaurace wa Isra’ila.

Wannan ya kuma sa Tlaib da Omar sun zamo ‘yan majalisun Amurka na farko da aka hana shiga Isra’ila.

Hakan ya sha banban da takwarorinsu 72 da suka shafe wata guda suna wata ziyara a Isra’ila wacce masu neman kamun-kafa suka shirya kuma suka dauki nauyi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Muftia Tlaib, wacce ke zaune a yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, ita ce kakar ‘yar majalisa Rashida Tlaib

Ilhan Omar da Rashida Tlaib suna shirin tashi zuwa Isra’ila ne domin shiga yankin Falasdinawa da ke karkashin mamayar Isra’ila: Gabashin Jerusalem da Yammacin Kogin Jordan.

Ga ‘yar majalisa Rashida Tlaib kuwa, tafiyar ta kunshi ziyarar danginta.

‘Yar majalisar mai shekara 42, lauya ce daga Michigan amma ‘yar asalin yankin Falasdinu, kuma har yanzu kakarta da sauran ‘yan uwanta na zaune a yankin na Falasdinu.

Bayan matakin na Isra’ila, Rashida Tlaib ta wallafa wani hoton kakarta a shafin Twitter, inda ta ce: “Matakin Isra’ila na hana jikarta, ‘yar majalisar wakilan Amurka, shiga kasar alama ce da ke nuna cewa halin da Falasdinawa ke ciki na tayar da hankali ne.”

Fafutukar ‘yancin bakar fata

Ta kuma misalta hakan da yadda aka taba hana mai fafutukar wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, wato fitaccen dan siyasa na Amurka Jesse Jackson.

Rashida Tlaib ta ce Isra’ila kasa ce ta “‘yan wariyar launin fata, abin da ita ma aka zarge ta da nuna “kin jinin Yahudawa”.

Hakkin mallakar hoto
GPO via Getty Images

Image caption

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka Donald Trump abokai ne sosai

Tana samun goyon baya a wannan fafutukar tata daga ‘yar majalisa Ihan Omar daga Minnesota, ‘yar shekara 38, wacce ke sanya dan kwali, ‘yar asalin Somaliya, wacce ta iso Amurka a 1995 a matsayin ‘yar gudun hijira.

Ta yi Allah-wadai da matakin hana su shiga Isra’ila, tana mai cewa abin kunya ne ga kasar da ke ikirarin cewa “ita kadai ce mai bin tafarkin demokuradiyya a yankin Gabas ta Tsakiya”.

Zargin kin jinin Yahudawa

An zargi Ilhan da nuna kin jinin Yahudawa bayan wasu kalamai da ta yi a baya, amma daga bisani ta nemi “afuwa” tana mai gode wa abokan aikinta kan yadda suka ja hankalinta kan irin munin kisan kare-dangin da aka yi wa Yahudawa.

Sannan ta ce ta yi niyyar sukar kungiyoyin Yahudawa ne da ke kamun kafa a fagen siyasar Amurka, ba wai Yahudawa gaba daya ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Falasdinawa sun ce kungiyar da ke neman a kaurace wa Isra’ila halattacciya ce kuma ba ta dauke da makamai – amma Isra’ila na musanta hakan

Mutumin da ya yi fice wurin sukar su shi ne Donald Trump, wanda shi ma ya nemi Isra’ila da ta hana su shiga kasar.

Trump ya bayyana ‘yan majalisar biyu da cewa “abin kunya” ne ga Amurka, sannan ya ce ba su izinin shiga kasar zai nuna gazawar Isra’ila.

“Sun tsani Isra’ila da dukkan Yahudawa, kuma babu wani abu da za a ce ko a yi da zai sauya zukatansu,” kamar yadda ya wallafa a Twitter.

Dokar hana kauracewa Isra’ila

Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce an yi amfani da dokar hana kaurace wa Isra’ila wurin hana ‘yan majalisar shiga kasar.

A karkashin dokar, wadda gwamnatinsa ta kafa a 2017, duk wani dan kasar waje da ya yi kiran a kaurace wa Isra’ila ta kowacce fuska – ba za a ba shi izinin shiga kasar ba.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

“Yan majalisar biyu sun musanta zargin cewa sun tsani Yahudawa

Isra’ila tana zargin kungiyar ta ‘yan a kaurace mata da cewa tana barazana ga dorewar kasar, matsayar da ‘yan siyasar Amurka da dama ciki har da ‘yan majalisar kasar na duka jam’iyyun biyu suka amince da su.

Sai dai duka bangarorin biyu sun yi watsi da batun cewa kiran a kaurace wa Isra’ila tamkar kin jinin Yahudawa ne.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

‘Zakzaky ya so kunyata Najeriya da Indiya a idon duniya’

Published

on

Ana tsare da Sheikh Zakzaky tun 2015

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce wasu dabi’u da shugaban kungiyar harka Isalamiyya na Najeriya ya nuna a kasar Indiya da ka iya kunyata gwamnatocin Najeriya da India na daga cikin dalilan da suka sanya aka mayar da shi gida.

A ranar Juma’a 16 ga watan Agusta ne dai Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya isa Najeriya bayan yunkurin kula da lafiyarsa da mai dakinsa Zeenat ya ci tura a kasar Indiya.

Malamin dai a cikin wani sako da ya fitar ta faifan bidiyo gabanin komawarsa Najeriya, ya ce yana ganin ba zai samu kulawar da ta dace ba, kasancewar ba a bar shi ya gana da likitocin da suka cancanta ba.

Sannan gabanin hakan ya yi zargin cewa an tsananta tsaro a asibitin da yake zaune, inda ya ce akwai matukar takura ga rayuwarsa.

Sai dai bayan komawar malamin Najeriya, kamfanin dillancin labaru na Najeriya ya ruwaito cewa babbar sakatariyar ma’aikatar yada labarun kasar, Mrs. Grace Gekpe ta ce halayyar da Sheikh Zakzaky ya nuna a kasar ta India ne ta sanya dole a mayar da shi gida.

A cewar wata sanarwar da ta fitar “A wani yunkuri na wancakali da ka’idoji na kasa da kasa, jagoran na IMN ya fara tuntubar wasu lauyoyi a Indiya da nufin neman mafaka a kasar”.

“Ya kuma tuntubi wasu kungiyoyi masu zaman kansu kamar hukumar kare hakkin dan’adam ta muslunci, da wasu kungiyoyi masu alaka da akidar Shi’a domin ganin ya samu nasarar neman mafakar”.

Sanarwar ta yi bayanin cewa inda Sheikh Ibrahim Zakzaky ya samu nasarar samun umurnin kotu a kasar Indiya na neman mafaka, to da hakan ya saba wa ka’idojin da kotu ta gindaya a Najeriya game da shari’ar da ake masa.

Bugu da kari sanarwar ta zargi matar Sheikh Zakzaky, Zeenat, da laifin kokarin haifar da rashin jituwa tsakanin jami’an tsaron Najeriya da na Indiya, a lokacin da ta zargi jami’an tsaron Najeriya da laifin kisan ‘yayanta.

Hakkin mallakar hoto
@SZAKZAKYOFFICE

Ita dai gwamnatin Najeriya ta yi kokarin bin umurnin wata babbar kotu ne ta jihar Kaduna, wadda ta amince wa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat su tafi kasar Indiya domin neman lafiya.

Malamin yana fama ne da rashin lafiya tun bayan kama shi da aka yi da matarsa a shekara ta 2015, bayan wani artabu tsakanin mabiya malamin da kuma jami’an tsaron Najeriya.

Sai dai an samu rashin jituwa bayan isar malamin kasar Indiya domin neman magani, inda malamin ya ki amincewa da likitocin da asibitin Medanta ta wakilta domin duba lafiyarsa.

Tun a shekara ta 2015 ne dai ake tsare da malamin, inda ake tuhumarsa da wasu jerin laifuka a gaban kotu.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Muhammad Jamal: ‘Abin da ya sa ake kirana Baturen Najeriya’

Published

on

Muhammad Jamal wanda aka fi sani da “White Nigerian” ya yi karin bayani a kan wannan inkiyar.

Ya bayyana cewa duk da launin fatarsa shi dan asalin garin Jos ne da ke tsakiyar Najeriya, amma kakansa na wajen mahaifiyarsa dan asalin kasar Lebanon ne kuma matarsa ‘yar Columbia ce.

Muhammad ya ce saboda hada dangi da mutane daban-daban za a iya kiran gidansu “Majalisar Dinkin Duniya. “

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: