HaÉ—arin jirgin ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 24 a Neja

A ranar Lahadin ne wani mummunan hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 24.

Gwamnan jihar Neja Mohammed Bago ya bayyana matukar kaduwarsa da faruwar lamarin kuma tun a lokacin ya yi kira da a dauki matakan kare lafiya cikin gaggawa.

Hadarin ya afku ne tsakanin karfe 7:30 na safe zuwa karfe 8:00 na safe a al’ummomin da ke tsakanin Jebba da madatsar ruwan Kainji. Yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da kananan yara.

Sama da mutane 30 ne aka ceto ya zuwa yanzu, sakamakon hadin gwiwar jami’an ‘yan sandan ruwa, masu ruwa da tsaki, da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja.

Gwamna Bago, a cikin wata sanarwa ta hannun babban sakataren yada labaransa, Bologi Ibrahim, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa.

More News

Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland. A ranar 22 ga watan Afrilu ne...

CBN ya dakatar da kudirinsa na sa bankuna su riƙa cajar kwastomominsu

Babban bankin Najeriya ya umarci bankunan da su dakatar da cajin kudaden ajiya har zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.Babban bankin ya bayyana hakan...

Ƴansanda sun kama likitan bogi

Rundunar ‘yan sanda ta Zone 2, Onikan, Legas, ta kama wani likitan jabu mai shekaru 37, kuma ma’aikacin lafiya, tare da zargin amfani da...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...