Gwamnonin PDP :Mun gamsu cewa Kotun Ƙoli Za Ta Yi Adalci A Shari’ar Zaɓukan Gwamnonin Zamfara Da Filato

Gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam’iyar PDP sun ce sun gamsu cewa kotun ƙoli za ta “yi adalci” a shari’o’in zaɓen gwamna da suka samu rashin nasara.

Matsayar gwamnonin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis a ƙarshen taron da suka gudanar a Abuja.

Gwamnonin sun ce sun tattauna kan abubuwa da dama da suke da alaƙa da su da kuma waɗanda suka damu kungiyar da suka haɗa da sake duba hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kan wasu zaɓukan gwamna da suka haɗa da na Zamfara da Filato

“A matsayin mu na kungiya muna sake jaddada kwarin gwiwar da muke da shi kan bangaren shari’a zai yi adalci,” a cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad.

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...