
Gwamnoni huɗu na jihohin arewa ta tsakiya sun bayar da tallafin miliyan N100 ga mutanen da rikicin jihar Filato na kwanan nan ya shafa.
A wata sanarwa ranar Talata, gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya ce shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Nasarawa,Abdullahi Sule shi ne ya sanar da haka a yayin wata ziyara a birnin Jos na jihar Filato.
Gwamnonin jihohin arewa ta tsakiya su huɗu sun kai ziyara jihar ne domin yiwa gwamnan jihar, Caleb Mutfwang jajen abin da yafaru.
Sama da mutane 100 ne aka kashe a wasu jerin hare-hare kan ayyuka 23 dake kananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi da kuma wani bangare na karamar hukumar Mangu a ranar 24 ga watan Disamba.
Alia ya bayyana damuwarsa kan yadda ake samun yawan hare hare kan manoma a jihohin arewa ta tsakiya.
A nasa bangaren gwamna, Caleb Mutfwang ya godewa gwamnonin kan ziyarar jajen da suka kawo masa.
Mutfawang ya ce yana fatan wata rana mutanen Najeriya za su taru a jihar Filato domin bikin taron murna farin ba na jimami ba.