A ranar Juma’a ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya yi wata ganawar sirri da gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Shugaba Tinubu a wani sako da ya wallafa a Facebook ya tabbatar da ganawar da gwamnonin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
“A yau na ji dadin tarbar fitattun Gwamnoni daga babbar jam’iyyar mu ta APC zuwa fadar gwamnati.
“Mun sake jaddada aniyarmu da kuma kokarin hada kanmu wajen ganin mun cimma kyawawan manufofinmu ga Nijeriya. Idanuka hada ƙarfi da karfe, za mu nasara wajen neman kasa mai wadata.” Ya buga
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ne ya jagoranci gwamnonin zuwa fadar gwamnatin, wanda kwanan nan ya karbi mukamin shugaban kungiyar Progressives Governors’ Forum, PGF.
Gwamnonin APC 17 daga cikin ashirin ne suka halarci taron.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo da Abiodun Abayomi Oyebanji na jihar Ekiti da kuma Dr Nasir Idris na jihar Kebbi da sauransu.