Gwamnatin Zamfara za ta bayar da tallafi saboda rage raɗaɗin matsin tattalin arziki

Gwamnatin jihar Zamfara ta bada izinin raba kayan abinci cikin gaggawa ga daukacin kananan hukumomin 14 a wani mataki na rage tasirin cire tallafin man fetur.

Matakin a cewar mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya nuna irin sadaukarwar da gwamnati mai ci ta yi na rage radadin kalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta.

Bala ya ce, “Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da a gaggauta raba kayan abinci a matsayin abin da zai rage wahalhalun da aka samu kai a ciko sakamakon cire tallafin man fetur.

“Kashin farko na rabon abinci zai fara ne da Shinkafa, Masara da sauransu.”

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...