Gwamnatin Zamfara ta yi gagarumin yunƙuri don magance matsalolin tsaro

Majalisar zartaswar jihar Zamfara ta amince da daukar mambobi 4200 aiki a rundunar hadin guiwa ta Civilian Task Force (JTF) don taimaka wa kokarin da hukumomin tsaro ke yi na magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Ma’aikatan na daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a taron SEC da Gwamna Dauda Lawal ya jagoranta, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar ranar Talata.

Taron ya kuma amince da gina sabbin ajujuwa, gyare-gyare da kuma kayyade kayayyakin makarantun a wani bangare na kudirin gwamnati na kara samun damar karatu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A kokarinsa na dakile matsalar rashin tsaro, Gwamna Dauda Lawal ya amince da daukar ma’aikatan civilian JTF a daukacin kananan hukumomin jihar.

“Yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwar jihar, Gwamnan ya kuma amince da gina sabbin ajujuwa, gyare-gyare da kuma samar da kayayyakin da ake da su a fadin kananan hukumomi 14 na jihar.”

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...