Gwamnatin tarayya za ta kawo karshen matsalar tsaro a watan Disamba

Gwamnatin Najeriya ta ci alwashin kawo karshen matsalar tsaro a cikin watan Disamba.

Ministan harkokin gida, Rauf Aregbesola shi ne ya sanar da haka.

Amma Aregbesola ya kalubalanci yan Najeriya da su taimakawa jami’an tsaro ta hanyar kai rahoton duk wasu ayyukan batagari da aka iya ta’azzara shaanin tsaro domin cimma wannan buri.

Ya kara da cewa tuni shirye-shirye sun yi nisa na samar da tsaro akan iyakokin kasarnan.

More from this stream

Recomended