Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Talata Da Laraba A Matsayin Hutun Sallah

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata da Laraba  matsayin ranakun hutun bukukuwan Ƙaramar Sallah.

Olubinmi Tunji-Ojo ministan harkokin cikin gida shi ne ya sanar da ranakun hutun a cikin wani saƙon taya murna ga Musulmin Naje da ya fitar ranar Lahadi.

Al’ummar Musulmi dake faɗin duniya baki ɗaya suke gabatar da bikin na Ƙaramar Sallah bayan kammala bikin watan Azumin Ramadana.

Ministan ya taya dukkanin al’ummar Musulmi murnar bikin sallar tare da yi musu addu’ar samun rahama Allah.

More from this stream

Recomended