
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a da kuma Litinin a matsayin ranakun hutu domin Musulmi su gudanar da shagulgulan karamar Sallah.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sahannun,Shuaibu Belgore babban sakataren ma’aikatar cikin gida.
Belgore ya ce ministan harkokin cikin, Rauf Aregbesola shi ne ya sanar da haka a ranar Laraba.