Gwamnatin Nijeriya Ta Rage Wa Manoma Farashin Takin Zamani – AREWA News

Gwamnatin Tarayya ta bayyana sanarwar rage farashin takin zamani samfurin NPK ga manoma, daga naira 5,500 zuwa naira 5,000 kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wannan sanarwa ta fito daga bakin Gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Samar da Takin Zamani na Shugaban Kasa.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Badaru ya ce gwamnati ta yi wannan rangwamen ne a lokacin ta na samar wa jama’a sauki daga kuncin da suke fuskanta dalilin barkewar Coronavirus a duniya.

Badaru ya ce an yi wa manoma da sauran masu amfani da takin zamani sasauci domin ganin cewa barkewar cutar Coronavirus bai yi wa harkar noma da manoma illa a a kasar nan ba.

Da ya ke magana a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, Badaru ya ce a za tabbatar da cewa an wadatar da takin zamani isasshe ga manoma nan da faduwar ruwan shuka ko saukar damina.

Ya ce kuma za a samar da taki samfurin wanda shi ne daidai da irin daminar yankin Arewa, wanda kuma ke da sinadari ingantacce da ba a yin algusshun sa.

A cikin jawabin Shugaba Muhammadu Buhari na ranar Litinin da ta gabata, ya bayyana cewa gwamnati za a yi kokarin tabbatar da cewa matsalar cutar Coronavirus ba ta yi wa harkar noma damina da na rani mummunar illa ba a shekarar 2020 da sauran shekaru masu zuwa.

Sai dai kuma manoma da dama sun raina ragin naira 500 kacal da gwamnati ta yi musu. Wasu na tunanin cewa naira 1,500 ya kamata a yi musu.

To in dai za a bi ana bai wa wasu naira 5,000 har naira 20,000 saboda Coronavirus, ina amfanin rage mana naira 500 kacal? Ragin naira 500 ai ko ni zan iya yi wa manoma shi.” Inji Nasiru, wani manomin albasa da ke Kano.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...