Gwamnatin Najeriya Da CNN Na Rigima

VOA Hausa

A karon farko, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fito ta yi Allah wadai, tare da kakaba takunkumi ga kafar yada labarai ta CNN, saboda rahotannin da ta bayar, da suka sa6a da abin da gwamnatin ta Najeriya ta ce su ne ainihin abubuwan da suka faru, lokacin zang zangar neman a rusa rundunar ‘yan sanda ta SARS.

Wanan na cikin bayanai ne da Ministan Yada Labarai da Al’adu na Najeriya, Lai Mohammed, ya yi wa manema labarai a Birnin Tarayya Abuja.

Korafe korafe da dama sun kunno kai da suka nuna barazana ga rayuka da aka yi wa masu zanga zangar da kafafen yada labarai daban daban suka yayata a wannan lokaci, amma daya daga cikinsu da ya fi daukar hankalin Gwamnati – da yake nuna sun take wasu ka’i’doji na yada labarai – shi ne gidan talabijin din CNN, wanda lai Mohammed ya ce dole a sa ma shi takunkunmi na musamman.

Lai Mohammed ya ce wakiliyar wata kafar yada labarai da ta ke wurin zanga zangar da aka yi a yankin kofar shiga Unguwar Lekki da ke lagos, ta bada rahoton zahirin abubuwa da suka faru, yayin da wakilan kafar yada labarai ta CNN suka fadi wani abu daban, inda suka nuna hotuna masu nuna cewa sojoji sun karkashe masu zanga zangar da dama, alhalin ba haka abin ya faru ba.

People hold banners as they demonstrate on the street to protest against police brutality, in Lagos, Nigeria, Tuesday Oct. 20, 2020. After 13 days of protests against police brutality, authorities have imposed a 24-hour curfew in Lagos, Nigeria's largest
People hold banners as they demonstrate on the street to protest against police brutality, in Lagos, Nigeria, Tuesday Oct. 20, 2020. After 13 days of protests against police brutality, authorities have imposed a 24-hour curfew in Lagos, Nigeria’s largest

Lai ya ce irin wadannan labarai da suka rika bazuwa ta yanar gizo da dandalin sada zumunta sun kara yayata wutar rikicin zanga zangar, har ya sa kasashe da dama, ciki har da Amurka, sun tofa albarkacin bakinsu a game da rahoton da kafar labarai ta CNN ta fitar.

To saidai mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya ce ko wace kafar yadda labarai ta na da matakan horarwa, saboda haka Gwamnati za ta jira ta ga irin matakin da za a dauka akan gidan talabijin din CNN, idan bai gamsar da Gwamnati ba, ita kanta Gwamnati za ta dauki mataki na aika wa mahukuntan Amurka takardar korafi domin su gyara.

Amma dan Majalisar Wakilai Mohammed Ali Wudil ya na ganin daukar matakin yin doka da za ta bada damar sa ido kan hanyoyin sadarwa zai yi wa kasa amfani.

FILE - Security guards walk past the entrance to CNN headquarters in Atlanta.
FILE – Security guards walk past the entrance to CNN headquarters in Atlanta.

In da yace dokar za ta rika duba yadda za a kula, ana gyarawa da inganta dandalin yanar gizon, ba wai ta yadda zai 6ata al’adu ko ya 6ata tarbiyya ko abubuwa na Najeriya ba.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya tsakanin gidan talabijin din CNN da Gwamnatin Najeriya, bayan an kammala bincike akan zanga zangar ENDSARS da abin da ya biyo baya.

More News

EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuÉ—aÉ—e

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa...

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...