Gwamnatin Najeriya ba za ta rufe ofisoshin jakadanci ba

Ofishin jakadancin Najeriya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ofishin jakadancin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotonnin da ke cewa za ta rufe wasu ofisoshin jakadancinta 80 cikin 110 da take da su a kasashen duniya.

A jiya ne dai aka tashi da rahotonnin cewa kasar na yunkurin rufe 80 daga cikin ofisoshin jakadancinta fadin duniya.

Rahotannin sun ce za ta rufe su ne saboda ba ta da halin ci gaba da gudanar da su. an kuma ce kasafin kudin baya-bayan nan ya ware kudin da za a gudanar da ayyukan ofisoshi talatin ne kawai.

To sai dai wani jami’an gwamnatin kasar ya ce rahoton ba shi da wani tushe ballanatana makama.

A ranar Laraba ne dai kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawan kasar ya bayyana cewa ofisohin jakadancin kasar a fadin duniya na cikin wani mummunan yanayi, inda kuma kwamitin ya zargi gwamnatin tarayyar kasar da yin watsi da su.

More News

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...