Gwamnatin Kebbi za ta kafa hukumar nakasassu

Gwamnatin jihar Kebbi ta ce za ta kafa hukumar nakasassu domin tabbatar da gudanar da su ma an dama da su a jihar.

Kwamishanan yada labarai da al’adu Alhaji Yakubu Ahmed ne ya bayyana hakan a Birnin Kebbi ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar, wadda Gwamna Nasir Idris ya jagoranta.

Ahmed ya ce an cimma matsayar kafa hukumar ne a taron da majalisar ta aike da kudirin ga majalisar jihar.

More from this stream

Recomended