Gwamnatin Kano za ta binciki masarautar Kano

Gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta sake dawo da batun binciken zargin yadda aka kashe kudade wajen tafiyar da Masarautar Kano, tun daga 2013 har zuwa 2019.

Hukumar Karbar Koke da Hana Rashawa ta Jihar Kano ta aika wa Masarautar Kano wasika a ranar 2 Ga Mayu, inda ta nemi wasu jami’an kula da tasarifin kudaden fadar su bayyana ofishin ta domin su yi karin bayani.

Babban jami’in hukumar mai suna Sulaiman Gusau ya sa wa Takardar hannu.

Wadanda aka gayyata sun hada da Babban Jami’in Kula da Harkokin Kudade, Mohammed Kawu, Shugaban Ma’aikata, Mannir Sanusi, Sakatare Isa Sanusi, wanda mahaifin su daya da Sarki. Sai kuma Mujitaba Falakin Kano.

Takardar ta ce zasu bayyana domin yin karin bayani a wasu wuraren da hukumar ke ganin an kauce Dokar Sashe na 26, wadda ta kafa Majalisar Masarautar Kano.

A gefe daya idan ba a manta ba, Majalisar Dokokin Kano na kokarin bijiro da dokar da za ta karkasa Masarautar Kano, da nufin Nada Sarki a Bichi, Gaya, Gwarzo da Rano.

Idan za a iya tunawa, tsohon gwamnan Jihar Kano, marigayi Abubakar Rimi, ya nada wasu sarakuna, sai dai Gwamna Sabo Bakin Zuwo na hawa, duk ya rusa su.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...