Gwamnatin Filato ta sanya dokar hana fita a Mangu saboda rashin tsaro

Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Mangu sakamakon hare-haren da suka kai ga asarar rayuka da dukiyoyi a yankin.

A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gwamnan, Gyang Bere ya sanya wa hannu, an dau matakin sanya dokar ta-bacin ne bayan tattaunawa da hukumar tsaro ta jihar da nufin maido da doka da oda a cikin al’ummomin da abin ya shafa.

Sakamakon dokar zaman gida, an hana zirga-zirga a cikin karamar hukumar har sai wani lokaci sai jami’an tsaro da masu gudanar da ayyuka masu muhimmanci yayin da aka umarci jami’an tsaro da su aiwatar da cikakken bin umarnin.

Gwamnan ya baiwa ‘yan jihar tabbacin tsaron rayuka da dukiyoyi da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar.

More from this stream

Recomended