Gwamnatin Borno Ta Wanke Wasu Mutane 500 Da Ake Zargin Su Da Hannu A Ayyukan Ta’addanci

Gwamnatin jihar Borno ta wanke wasu mutane  daga zargin da ake masu na hannu a ayyukan ta’addanci a jihar.

Kafin a wanke mutane daga dukkanin zargin da ake masu ana tsare da su ne a barikin sojoji ta Giwa dake Maiduguri.

Kamfanin Dilalancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa kwamishiniyar mata ta jihar Borno,Zuwaira Gambo ita ta sanar da haka a ranar Laraba da take jawabi ga wasu  mata da suka gudanar da zanga-zanga.

Hajja Gana wacce ke jagorantar matan ta yi zargin cewa sojoji suna cigaba da tsare yaransu da basu aikata laifin komai ba.

Gambo ta ce an saki waɗanda ake zargin rukuni rukuni inda aka miƙawa gwamnatin jihar Borno su.

“Rukunin ƙarshe  sune mutane 28 da aka saka makon da ya wuce,” ta ce.

Gambo ta tabbatarwa da waɗanda ƴan uwansu suke tsare a hannun sojoji kan rikicin Boko Haram da kada suji tsoro matuƙar sun tabbatar da cewa basu aikata laifin komai ba.

Kwamishiniyar ta ce gwamnati na aiki kafaɗa da kafaɗa da sojoji domin ta tabbatar da cewa anyi adalci ga kowa.

More from this stream

Recomended