Gwamnatin Bauchi Ta Raba Wa Kananan Hukumomin Jihar Na’urar Tiransifoma Sama Da Sittin

Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed A. Abubakar, ya kaddamar da rabon na’urar samar da wutan lantarki na (Transformer) har sama da sittin, mai karfin kba 500 ga kananan hukumomin jihar guda 20.

An kaddamar da rabon ne a sakateriyar gwamnatin jihar Bauchi.

Gwamna M.A ya shaidawa Shugabannin kananan hukumomin jihar Bauchi cewa alhakin sayan na’urar samar da wutar lantarki ba yana kan gwamnati bane, ya yi hakan ne domin cire talakawan jihar daga matsalolin wutar lantarki da suke fama da shi.

Gwamnan ya kuma ja kunnen shugabannin kananan hukumomin da su kula da na’urorin dan gudun barnatawar.

Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Bauchi (ALGON) Shugaban karamar hukumar Katagum ya yi godiya ga Gwamna M.A kan irin wannan kulawa da talakawa da gwamnatinsa me yi, ya sha alwashin kulawa da wadannan na’urar da gwamnatin ta samar musu da shi. Ya ce za su tabbatar da cewa jama’ar su sun amfana da na’urar ta inda ya da ce.

Mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi kan Sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar, ya bayyana cewa
kowace karamar hukuma za ta samu nauran bada wutar guda uku ne cikin dukkanin kananan hukumomin jihar Bauchi..

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Ƴansanda sun kama wanda ya kitsa harin da aka kai wa jirgin ƙasa a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Alhamis, ta sanar da kame wanda ake zargin ya shirya harin da aka kai a jirgin ƙasan Abuja-Kaduna...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...