Gwamnati ta yi sakaci kan matsalar tsaro a Najeriya- PDP

tutar jam'iyyar PDP

Hakkin mallakar hoto
BUZZ NIGERIA

Babbar jam’iyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce matsalolin da al’ummar kasar ke fuskanta ta bangaren tsaro a yanzu ba ya sa rasa nasaba da yadda gwamnati ke tafi da mulki.

Sanata Umaru Tsauri, sakataran kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana haka a wata hira da yayi da BBC.

Ya ce rashin fadar gaskiyar lamurra game da halin da kasa ke ciki daga bangaren gwamnati na daya daga cikin dalilan da suka jefa kasar cikin halin rashin tsaron da take ciki.

Ya ce “babu abin da ya jawo wannan matsala illa gwamnati ta ki yarda ta fadi wa mutane gaskiya cewa wannan abu na faruwa, kuma a dauki mataki.”

Ya kuma ce aikin gwamnati ne ta gano wadanda ke da hannu cikin abubuwan da suka jawo tabarbarewar tsaro a Najeriya, ba jama’ar kasar ba.

Sanata Umaru Tsauri ya ce halin da Najeriya ta shiga ba ya yi wa su kansu ‘yan adawa dadi saboda lamari ne da ya shafi kowa a kasar.

“Mu ‘yan adawa abin da muke so shi ne a gamsu, a yarda cewa abubuwan da ke faruwa sun shafi mutane, kuma mutanen nan lallai ne a yi abinda aka tsayar da abin da ke faruwa gare su,” a cewarsa.

Ya ce abin yi yanzu shi ne gwamnati ta binciko tushen matsalar, sannan ta yarda cewa matsalar ta fito fili sannan ta nemi maganinta ta hanyar amfani da dimbin mutanen da ke cikin gwamnati.

“A kullum gwamnati na nuna cewa tashin hankalin bai kai yadda ake tsamanninsa ba, don kuwa a kullum wadanda ake garkuwa da su talakawa ne.” in ji Sanata Tsauri.

Ya ce idan aka sace wani babba a gwamnati ba a sakin jiki, don haka me zai hana ba za a dauki irin wannan matakin ba a kodayaushe?

Matsalar tsaro, musamman ta garkuwa da mutane don karbar kudin fansa a arewacin Najeriya ta zama daya daga cikin manyan matsalolin da kasar ke fuskanta a halin yanzu kuma kalubale ga gwamnati mai ci.

More News

Mutane uku sun mutu a ruftawar wani ginin bene a Kano

Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ta Ƙasa NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane uku bayan da wani bene mai hawa uku ya ruguzo a unguwar...

Ganduje Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Shirya Zanga-Zangar Neman A Sauke Shi

Shugaban jam'iyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin jihar Kano ta jam'iyar NNPP ita ce ke da alhakin shirya zanga-zanga iri...

Qatar za ta taimaki marayu a Najeriya

Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana cewa za ta ba da tallafi ga yara marayu sama da 1,000 da suka rasa iyayensu saboda rikicin Boko...

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...