Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya kai ziyara wasu sassan jihar da ambaliyar ruwa tayi mummunan barna.
A yayin ziyarar gwamnan ya jajantawa al’ummar garin Jumbam inda aka rasa rayukan mutane 10 a wani hatsarin jirgin ruwa.
Garuruwan Jumbam da Kaliyari dukkansu a karamar hukumar Tarmuwa na daga cikin inda ambaliyar ruwan tayi wa mummunan barna.
Har ila yau gwamnan ya bayar da umarnin gaggauta sake gina titunan da ambaliyar ruwan ta lalata.



