Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya fara biyan alawus-alawus na N6,500 duk wata ga masu fama da nakasa a jihar.
Sakataren yada labarai na gwamnan, Malam Abubakar Bawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya kara da cewa an fara biyan kudaden ne a ranar Talata a cibiyoyi uku na kananan hukumomin Sokoto ta Arewa, Dange Shuni da Gwadabawa na jihar.
Ya ce shirin ya samu tarin mutanen da aka riga aka tantance, wadanda suka karbi Naira 6,500 kowanne a matsayin alawus din su na wata-wata.
Sanarwar ta ruwaito wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin sun yaba wa gwamnan kan maido da alawus alawus din na wata.
Sun ce hakan zai bi su wajen inganta rayuwarsu, baya ga rage barace-barace a kan tituna.