
Gwamnonin jam’iyar PDP za su gudanar da wata ganawa ranar Talata domin tattauna halin da al’amura ke gudana a Najeriya.
A cikin wata sanarwa ranar Litinin dake sanar da taron, Cyril Maduabum darakta janar na kungiyar gwamnonin jam’iyar PDP ya ce za kuma a tattauna halin da jam’iyar take ciki.
Maduabum ya ce taron wanda shi ne karo na farko tun bayan gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ya karbi ragamar jagorancin kungiyar gwamnonin za a gudanar da shi a masaukin baki na gwamnatin Akwa Ibom dake Abuja.
“Ana sa ran kungiyar za ta tattauna kan halin da kasa ke ciki musamman abubuwan dake faruwa a yan kwanakin nan ta bangaren siyasa, zamantakewa da kuma tattalin arziki,” a cewar sanarwar.